Babbar magana: Masoyan wata fitacciyar jarumar fim sun bukaci ta koma yin fina-finan batsa bayan ta wallafa wasu hotuna
- Masoyan fitacciyar jarumar nan ta masana'antar Nollywood mai kyakyawar sura, Molo Lawal, sun shawarceta da ta fada masana'antar fina-finan batsa
- Masoyan nata sun bata shawarar ne sakamakon yadda tayi bayyana dirarren jikinta a hotunan da take sanyawa a kafafen sada zumunta
- Jarumar ta ce, maganar da masoyan nata suka yi bai dame ta ba domin ta dauki maganar ne a matsayin yabo
Fitacciyar jarumar nan ta masana'antar Nollywood mai dirarriyar sura wato Moyo Lawal, ta mayar da martani akan wata magana da masoyanta suka yi a kanta
Biyo bayan wallafa wasu hotuna a shafukanta na sada zumunta da suke nuni da surarta, masoyanta da yawa a cikin watannin nan sun bata shawartar da ta fada masana'antar shirya fina-finan batsa.
A mayar da martanin da jaruma Moyo Lawal tayi, ta ce wadannan tsokacin da masoyantan suka yi ta daukesu ne a matsayin yabo gareta.
A wani bayani kuma da jarumar tayi, tace ta gaji da bayyana a matsayin ta gari a fina-finai. Ta bukaci jama'a da su banbance dabi'arta a fina-finai da kuma asalin halayyarta.
KU KARANTA: Jamila Nagudu ce tafi cancanta a bawa gwarzuwar shekara ba Fati Washa ba - In ji Kamaye na Dadin Kowa
"Idan kun taba ganina ina busa hayaki a wasan kwaikwayo, zaku iya cewa ni kwararriya ce, amma a gaskiya bana shan hayaki," in ji ta.
"Na san ba kowane zai yadda da abinda na fada ba, ni a wurina, dole ne wasan kwaikwayona ya nuna kamar da gaske ne. Duk da nakan ji haushi idan mutane basu iya banbance wasan kwaikwayo da asalin halayyata, amma ina tsananin jin dadi da irin kwarewa ta da har mutane basa iya banbance halina," in ji jarumar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng