Ironsi: Iyalan Marigayin Sun Nemi Diyya Bayan Shekaru 58 da Kashe Shi a Juyin Mulki
- Iyalan tsohon shugaban mulkin soja na farko, Janar Johnson Aguiyi-Ironsi, sun bukaci gwamnatin tarayya ta ba su hakuri da diyya
- Imo Aguiyi-Ironsi ya ce marigayin ba shi da hannu a juyin mulkin Janairun 1966, sai dai mukaminsa ne ya jawo aka kashe shi
- Iyalan sun bukaci sulhu na gaskiya, suna mai cewa Aguiyi-Ironsi jagora ne mai hangen nesa wanda aka zalunta duk da rashin aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia - Iyalan tsohon shugaban mulkin soja na farko a Najeriya, Janar Johnson Aguiyi-Ironsi, sun tura bukata ta musamman ga gwamnatin tarayya.
Iyalan sun bukaci gwamnatin tarayya ta ba su hakuri bisa kashe shi a shekarar 1966. Sun kuma nemi a biya su diyya tare da samar da sulhu na gaskiya.

Source: Getty Images
Bukatar iyalan Aguiyi-Ironsi ga gwamnatin tarayya
Shugaban iyalan, Imo Aguiyi-Ironsi, ya bayyana hakan yayin wata hira da Arise News, ya ce iyalansu na bukatar cikakken uzuri, diyya da kuma sulhu domin rufe wannan babi na tarihi.
A cewarsa, marigayin kawunsa jagora ne mai hangen nesa, mai son hadin kan Najeriya kuma wanda bai nuna bambancin kabila ba. Ya ce ya yi wa kasa hidima cikin gaskiya.
Ya kara da cewa Aguiyi-Ironsi ya shafe watanni shida kacal yana shugabancin kasa kafin aka kashe shi. Ya ce ba saboda wani laifi da ya aikata ba ne aka kashe shi.
Imo ya jaddada cewa marigayin ba shi da hannu a juyin mulkin Janairun 1966, kuma wannan gaskiya ce da kowa ya sani. Ya ce mukaminsa ne a matsayin babban hafsan soja ya jefa shi cikin hadari.
Ya bayyana cewa saboda kasancewarsa babban jami'in soja aka dora masa jagorancin kasa bayan juyin mulkin, kuma wannan ne daga bisani ya jawo aka kashe shi.
Ya bayyana fatan cewa masu ikon daukar mataki za su saurari wannan kira, su ba iyalansu hakurin da suka dade suna jira tare da daukar matakan sulhu.

Source: Twitter
Lokacin da Aguiyi-Ironsi ya mulki Najeriya
Aguiyi-Ironsi ya shugabanci Najeriya daga 16 ga Janairu zuwa 29 ga Yulin 1966 bayan juyin mulkin da ya kashe shugabannin siyasa da dama a kasar.
Ko da yake ya tsallake rijiya da baya a juyin mulkin farko, matakinsa na mayar da iko hannun gwamnatin tarayya da kuma rashin hukunta masu juyin mulkin ya haifar da rashin jin dadi.
A ranar 29 ga Yulin 1966, wasu sojojin Arewa suka kashe Aguiyi-Ironsi tare da mai masaukinsa, Laftanar Kanar Adekunle Fajuyi, a juyin mulkin ramuwar gayya da ya canja alkiblar siyasar Najeriya.
Wasu ranaku da suka sauya tarihin Najeriya
A baya, mun ba ku rahoton cewa a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966, aka yi juyin-mulkin farko a Najeriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shugabannin da ke mulki a wancan lokaci.
A wannan rana wasu sojoji masu dumin-kirji, wanda kusan dukkanninsu sun fito ne daga kabilar Ibo ne, suka hambarar da gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa.
Wadanda suka jagoranci wannan danyen aikin kashe Firayim Minista da Firimiyoyin larduna su ne: Chukwuma Kaduna Nzeogwu da Emmanuel Ifeajuna.
Asali: Legit.ng

