Zargin Almundahanar Kudi: An Fara Shirin Tsige Kakakin Majalisa a Najeriya
- Akalla 'yan majalisar Ondo 24 sun bayyana goyon bayansu ga shirin tsige kakakin majalisar, Olamide Oladiji, bisa zargin almundahanar kuɗaɗe
- Masu neman tsige kakakin sun ce ya rasa amincewar mafi yawan mambobin majalisar duk da ƙoƙarin sulhun da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi
- Kakakin majalisar ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa rikicin na da alaƙa da siyasar zaɓen 2027 ba wai batun almundahanar kuɗi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Odo - Rikicin shugabanci da ya dabaibaye Majalisar Dokokin Jihar Ondo ya ƙara tsananta bayan rahotanni sun nuna cewa 'yan majalisa 24 daga cikin 26 sun bayyana goyon bayansu ga shirin tsige kakakin majalisar, Rt. Hon. Olamide Oladiji.
Ana zargin kakakin da almundahanar kuɗi da kuma amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba, musamman kan batun kusan Naira miliyan 44 da ake alaƙanta da sake tsara kasafin kuɗin Hukumar Raya Yankunan Masu Arzikin Mai ta Jihar Ondo (OSOPADEC).

Source: UGC
'Yan majalisa sun dage kan tsige kakakinsu
Sabon ci gaban ya zo ne duk da ƙoƙarin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa da shugabannin jam'iyyar APC suka yi na sasanta rikicin da ya kunno kai a majalisar, in ji rahoton Vanguard.
Da take magana a madadin 'yan majalisar da ke neman tsige kakakin, Hon. Olawunmi Fayemi-Obayelu, mai wakiltar mazaɓar Ilaje II, ta bayyana cewa ƙarin 'yan majalisa uku sun shiga cikin waɗanda suka amince da shirin tsige Olamide Oladiji.
A cewarta, hakan ya nuna cewa kakakin ya rasa amincewar mafi yawan mambobin majalisar, lamarin da ya sa ci gaba da zamansa a kan kujerar shugabanci ya zama abin tambaya.
Ta kuma zargi kakakin da fitar da wasu kudurorin majalisa ba tare da samun amincewar mambobin majalisar ba.
Hakazalika, ta nuna damuwa kan yadda aka gudanar da rabon mitocin lantarki a ƙarƙashin shirin O'Datiwa Meter Distribution Programme na gwamnatin jihar.
A cewarta, idan kakakin ya sauka daga mukaminsa, hakan zai taimaka wajen kare mutuncin majalisar da kuma sunansa.
Kakakin majalisa ya yi watsi da zarge-zarge
A nasa martanin, Rt. Hon. Olamide Oladiji ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Ya bayyana yunƙurin tsige shi a matsayin wani shiri na siyasa da ke da alaƙa da shirye-shiryen zaɓen shekarar 2027, ba wai saboda zargin almundahanar kuɗi ba.
A cewarsa, wasu daga cikin 'yan majalisar da ke jagorantar yunƙurin sun nuna rashin jin daɗi ne bayan sun kasa samun tikitin sake tsayawa takara.
Ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikinsu ba su gamsu da goyon bayan da yake samu na ci gaba da zama kakakin majalisar ba.
Shugaban kwamitin ya mayar da martani
Jaridar Punch ta rahoto cewa, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Hon. Olatunji Fabiyi, ya yi watsi da bayanan kakakin.

Source: Original
Ya ce batun tsige shi ya samo asali ne daga matsalolin shugabanci da kuma buƙatar tabbatar da gaskiya da riƙon amana a majalisar.
Fabiyi ya zargi kakakin da sake tsara kasafin kuɗin OSOPADEC ba tare da sahalewar majalisar ba, yana mai cewa hakan ya saɓa wa ƙa'idojin gudanar da harkokin majalisa.
Ya jaddada cewa matsayar mafi yawan 'yan majalisar ba ta sauya ba, duk da ƙoƙarin sulhu da gwamnati da shugabannin APC ke yi.
Yayin da wa'adin sulhun ke dab da ƙarewa, ana sa ran makomar kakakin majalisar za ta bayyana nan ba da jimawa ba idan bangarorin suka kasa cimma matsaya guda.
An hurowa shugaban majalisa wuta
A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan Majalisar Dokokin Jihar Ondo 21 daga cikin 26 sun rattaba hannu kan takardar tsige kakakin majalisar, Olamide Oladiji, kan zargin almundahanar kuɗi.
Sun zargi Kakakin da karkatar da Naira miliyan 44 da aka ware domin sake tsara kasafin kuɗin Hukumar Raya Yankunan Masu Hakar Mai ta Jihar Ondo (OSOPADEC).
A nasa martanin, lokacin da aka tuntube shi ta waya, Kakakin Majalisar da ke fuskantar matsin lamba ya musanta zarge-zargen.
Asali: Legit.ng


