Yanzu-yanzu: An saki ASD, 'Dansa, Surukinsa, da Sheikh Murtala Al-Misry

Yanzu-yanzu: An saki ASD, 'Dansa, Surukinsa, da Sheikh Murtala Al-Misry

Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta saki shahrarren dan kasuwa kuma tsohon shugaban kamfanin motar Peugeot Automobile Nigeria Ltd., PAN, Alhaji Sani Dauda ASD, bayan an tsareshi kan aurar da diyarsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyarmu ta bayyana cewa Alhaji Sani Dauda, dansa, sabon angon Abdullahi Kumali da Alkalin kotun shari'a, Sheikh Murtala Nasir Al-Misry, sun isa gida misalin karfe 8:30 na safe.

Mun kawo muku rahoton cewa jami’an Yansanda dake yaki da yan fashi da makami na rundunar Yansandan Najeriya sun kama Alhaji Sani Dauda a kan rikici daya biyo aurar da diyarsa da ya yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito surukin ASD, kuma tsohon mijin diyarsa Naseeba ne ya umarci Yansanda su kama Alhaji Sani Dauda, tare da dansa Shehu Dauda da kuma alkalin kotun Musulunci dake Magajin gari, Murtala Nasir, wanda shi ne ya daura auren Naseeba da wani sabon miji.

KU KARANTA: Gab da zabe, Surukin Atiku ya bani $140,000 in kaiwa Osinbajo - Shaida a kotu

Majiyarmu ta ruwaito an daura auren Naseeba da wani mijin ne a ranar Asabar, 9 ga watan Nuwamba, wanda hakan ya matukar bata ma tsohon mijinta rai, da wannan yasa Yansanda suka kama masa mahaifinta da sauran mutanen biyu a ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel