Alkalin Alkalai Ta Hana Lauyoyi Amfani da ‘Barista’ a Farkon Sunayensu Gaba Daya
- Alkalin Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayar da umarni ga lauyoyi kan amfani da sunan 'barista'
- Umarnin ya shafi duk lauyoyi, magatakardan kotu da ma’aikata, inda aka ce lakabin bai dace da ƙa’idojin ƙwarewar Kotun Koli ba
- Kotun Koli ta ce sabon matakin zai daidaita takardu a hukumance tare da tabbatar da bin ƙa’idojin aiki iri ɗaya tsakanin lauyoyi da ma’aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Alkalin Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta kawo wata doka musamman domin lauyoyi a kasar.
Alkalin alkalan ta umarci lauyoyi da ma’aikatan kotu su daina amfani da lakabin “barista” a farkon sunayensu a duk wata mu’amalar a hukumance da Kotun Koli.

Source: Twitter
Umarnin da alkalin alkalai ta bayar
An bayyana umarnin ne a cikin wata takarda mai ɗauke da ranar 13 ga Yulin 2026, wadda Babban Magatakardan Kotun Koli, Kabir Akanbi, ya sanya wa hannu, cewar Punch.
Ta bayyana cewa ci gaba da amfani da wannan lakabi bai dace da ƙa’idojin ƙwarewar aiki da Kotun Koli ke son tabbatarwa a dukkan harkokinta a hukumance ba.
Sabon umarnin ya fara aiki nan take, kuma ya shafi lauyoyi masu shari’a, magatakardan kotu, ma’aikatan sashen shari’a da duk wani lauya da ke hulɗa da Kotun Koli.

Source: Facebook
Musabbabin hana lauyoyi amfani da 'barista'
A cewar takardar, Alkalin Alkalai ta yanke hukuncin cewa amfani da kalmar “barista” a matsayin lakabi kafin suna bai dace da matsayin ƙwarewar da ake buƙata ba.
Saboda haka, an umurci dukkan waɗanda abin ya shafa su daina amfani da lakabin a wasiƙu, takardun kotu, bayanan hukuma, katunan shaida da sauran mu’amaloli a hukumance cikin gaggawa.
Takardar ta kuma umurci shugabannin sassa da na rukunoni su tabbatar da cewa duk ma’aikatan da ke ƙarƙashinsu sun aiwatar da wannan umarni ba tare da ɓata lokaci ba, cewar TheCable.
Wannan na daga cikin sababbin matakan gudanarwa da Mai Shari’a Kekere-Ekun ta ƙaddamar tun bayan hawanta shugabancin bangaren shari’a a Najeriya.
A fannin shari’a, kalmar “barista” na nufin lauya mai cancantar gabatar da ƙara a manyan kotuna, amma a Najeriya ana yi wa lauyoyi rajista a matsayin barista da 'Solicitors' na Kotun Koli.
Duk da cewa wasu lauyoyi suna amfani da lakabin ne da son rai, wasu kuma suna amfani da sunayensu tare da cancantunsu kamar SAN, PhD da sauran manyan matakan ƙwarewa, yayin da sabon umarnin zai daidaita tsarin takardu a hukumance a Kotun Koli.
Yan bindiga sun sace babban alkali
An ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza.
Hatsabiban 'yan bindigan sun yi awon gaba da shi daga gidansa da ke kan titin Zogirma a ƙaramar hukumar Bunza.
Rundunar ’yan sanda ta tura jami’an leƙen asiri da na musamman domin ceto alkalin wanda ya fada komar 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng

