Babbar Magana: Iran Ta Jawo Matsala da Trump Ya Yi Sabuwar Barazana
- Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da kai wa Iran hare-hare masu tsanani a cikin makonni huɗu masu zuwa
- Ya yi ikirarin cewa hare-haren sun raunana karfin sojin Iran, yana mai cewa kasar ta rasa manyan rundunoninta
- Shugaba Trump ya kuma ce an samu fahimtar juna da Isra’ila kan shirin kwance damarar Hamas ta hanyar ajiye makamansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce Washington za ta ci gaba da kai wa Iran hare-hare masu tsanani, yayin da rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ke ci gaba.
Shugaba Trump ya kuma yi ikirarin cewa Iran ta rasa karfinta, inda ya ce ba ta da rundunonin sojojin kasa, ruwa da na sama.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce Trump ya bayyana hakan ne yayin wani taron majalisar ministocinsa a ranar Juma'a, 31 ga watan Yulin 2026, inda ‘yan jarida suka tambaye shi abin da yake sa ran gani a cikin makonni huɗu masu zuwa.
Shugaba Trump ya ka da baki ya ce:
“Za mu kai wa Iran hare-hare masu tsanani.”
Trump ya kara da cewa a wani lokaci Iran za ta ce ba za ta iya jurewa ba.
“A wani lokaci, za su ce ba za mu iya jurewa kuma ba.”
- Shugaba Trump
Trump ya ce Iran ta rage karfi
Da aka tambaye shi game da yiwuwar dawo da yarjejeniyar tsagaita wuta bayan hare-haren da Amurka da Iran suka rika kai wa juna, Trump ya ce burinsa shi ne samun nasara.
“Muna yin abin da ya dace sosai. Muna kokarin nuna sauki gwargwadon yadda zai yiwu a irin wannan yanayi, amma kun san ana matukar ragargaza su.”
- Shugaba Donald Trump
Trump ya yi ikirarin cewa Iran ba ta da rundunar ruwa, rundunar sama ko kuma ingantaccen tsarin kariya daga hare-haren sama.
Sai dai ya ce har yanzu kasar tana da wasu karfi, ko da yake bai bayyana su da yawa ba.
“Wannan ba yana nufin ba su da wani karfi ba. Suna da wasu karfi, amma kadan ne.”
- Shugaba Donald Trump
“Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba”
Trump ya jaddada cewa Amurka ba za ta amince Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.
“Abin yana da sauki. Ba za su iya mallakar makamin nukiliya ba. Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, kuma ba za su iya mallakarsa ba.”
- Shugaba Donald Trump

Source: Getty Images
Ya yi ikirarin cewa da Iran ta mallaki irin wannan makami, da tuni an lalata yankin Gabas ta Tsakiya.
“Da sun mallake shi, da an shafe Gabas ta Tsakiya.”
- Shugaba Donald Trump
Iran ta lalata jiragen yakin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta lalata jiragen yaƙin F-35 guda uku na Amurka.
Rundunar IRGC ta kuma bayyana cewa ta yi wa wasu jiragen guda uku mummunar ɓarna a wani hari da ta kai sansanin sojojin sama na al-Azraq da ke kasar Jordan.
Asali: Legit.ng

