Matsalar tsaro: An fara yi ma bakin haure rajista a jahar Sakkwato

Matsalar tsaro: An fara yi ma bakin haure rajista a jahar Sakkwato

Gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da aikin tantancewa tare da yi ma bakin haure mazauna jahar Sakkwato rajista tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Gwamna Tambuwal ya bayyana aikin a matsayin wanda ya kamata duba da matsalolin tsaron da ake yawan samu a jahar da sauran sassan kasar Najeriya.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojan sama sun tarwatsa mafakar Boko Haram, sun kashe da dama

Sakataren gwamnan jahar Sakkwato, Alhaji Sa’idu Ubandoma ne ya wakilci Gwamna Tambuwal a yayin taron kaddamar da aikin, inda yace gwamnati ta damu kwarai game da sa hannun bakin haure cikin tayar da zauni tsaye a Najeriya ta hanyar miyagun ayyuka.

Don haka gwamnan ya yi kira ga bakin haure su baiwa gwamnati hadin kai domin gudanar da wannan muhimmin aiki cikin nasara, inda ya jaddada musu muhimmancin aikin, musamman a garesu, saboda basu karin kariya.

A nasa jawabin, shugaban hukumar shige da fice na Najeriya reshen jahar Sakkwato, Muhammad Hassan ya bayyana cewa an kirkiro matakin ne domin karfafa tsaro a jahar, saboda a cewarsa mutanen da ba yan Najeriya ba suke kitsa matsalolin tsaro a Najeriya.

Haka zalika yace hukumar ba za ta caji kowa ko sisi ba, don haka kyauta ne, kuma zasu fadada aikin zuwa kananan hukumomin jahar guda 23. Bugu da kari Muhammad ya nemi dukkanin mutanen da bakin haure ke musu aiki su tabbata sun kaisu an musu rajista.

A wani labarin kuma, miyagun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun halaka wani mutumi mai suna Hamza Abubakar Mahuta bayan sun karbi kudin fansa daga hannun yan uwansa, kudin da ya kai naira dubu 500.

Majiyarmu ta ruwaito Hamza Mahuta jami’i ne hukumar kula da dokokin hanya ta jahar Kaduna, wanda yan bindigan suka yi awon gaba da shi a ranar 16 ga watan Oktoba a kan hanyar Birnin Gwari yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida wajen iyalansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel