Obasanjo Ya Kama Sunan Atiku da Ya Ambaci Babban Kuskuren da Ya Yi Rayuwa
- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce zaben Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a 1999 shi ne babban kuskuren da ya taba yi a rayuwarsa
- Obasanjo ya ce da zai sake samun dama, ba zai zabi Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa ba
- Tsohon shugaban kasar ya ce duk da sabanin da suka samu, bai bari hakan ya hana shi gudanar da mulkin Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan babban kuskuren da ya taba yi a rayuwarsa.
Obasanjo ya bayyana cewa zaben Alhaji Atiku Abubakar a matsayin mataimakinsa a zaben shugaban kasa na 1999 shi ne babban kuskuren da ya taba yi a rayuwarsa.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Obasanjo ya fadi hakan ne ranar Juma’a, 31 ga watan Yulin 2026 a Legas yayin wata tattaunawa da fitaccen mawaki kuma mai fafutuka, Charly Boy.
An shirya taron ne domin kaddamar da gidauniyar Charly Boy da kuma littafin tarihinsa mai taken '999: A Memoir in Tribute to Late Justice Chukwudifu Oputa.'
Obasanjo ya yi magana kan Atiku
Tsohon shugaban kasar ya ce idan zai sake komawa baya, ba zai zabi Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasa ba.
“Zan ce babban kuskuren da na yi shi ne zaben Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kasa na a 1999.”
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya kara da cewa yana godiya ga Allah saboda bai bari abubuwan da Atiku ya yi da yadda ya rika mayar da martani sun kawo cikas ga gwamnatinsa ko suka dauke masa hankali daga gudanar da mulkin kasar ba.
“Babu wani bacin rai a zuciyata kan abin da ya faru. Duk da komai, na samu nasarar cimma abubuwan da na sanya a gaba yayin da nake kan mulki.”
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya yi bayani kan asalinsa
Tsohon shugaban kasar ya kuma yi magana kan cece-kucen da aka dade ana yi game da asalinsa. Ya bayyana cewa iyayensa ‘yan Abeokuta ne, babban birnin jihar Ogun.
“Har yanzu na san gidan danginmu da ke can.”
- Olusegun Obasanjo
Manyan mutane sun halarci taron
Taron ya samu halartar manyan mutane da suka hada da tsohon babban sakataren kungiyar Commonwealth, Cif Emeka Anyaoku.
Sauran wadanda suka halarta sun hada da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar National Democratic Congress (NDC), da hamshakin dan kasuwa, Leo Stan Ekeh.
Leo Stan Ekeh ya bayar da gudummawar Naira miliyan 20 a madadin Obasanjo, sannan ya bayar da irin wannan adadin a madadin Cif Emeka Anyaoku.
Hakazalika nazarin littattafai, Dakta Austin Tam-George, da fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin, Bisi Olatilo, tare da wasu manyan baki sun halarci taron.

Source: Twitter
Dangantakar Obasanjo da Atiku
Obasanjo da Atiku sun tsaya takarar shugaban kasa da mataimakinsa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Sun jagoranci Najeriya daga 1999 zuwa 2007.
Sai dai dangantakarsu ta yi tsami daga baya sakamakon sabanin siyasa da suka samu a wa’adinsu na biyu a mulki.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su
Atiku ya yi wa Obasanjo martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi martani ga Olusegun Obasanjo.
Atiku ya yi watsi da sabon zargin da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi masa kan yunkurin tsige shi.
Asali: Legit.ng

