An Kama Dan Shekara 20 Da Zargin ba 'Yan Bindiga Makamai
- Rundunar 'yan sandan jihar Benue ta kama wani matashi mai shekara 20 da ake zargin yana kai wa 'yan bindiga alburusai a ƙaramar hukumar Guma
- An kama wanda ake zargin ne da alburusai da suka kai 115 bayan ɗaya daga cikin mutanen da suke tare ya tsere zuwa cikin daji
- Rundunar ta ce ta fara bincike domin gano inda aka samo alburusan da kuma inda za a kai su, yayin da ake neman wanda ya tsere ido rufe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Makurdi – Rundunar 'yan sandan jihar Benue ta sanar da cafke wani matashi mai shekara 20 da ake zargin yana safarar alburusai ga 'yan bindiga a ƙaramar hukumar Guma.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Peter Aondona, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma'a.

Source: Original
Punch ta rahoto cewa an kama wanda ake zargin ne yayin wani samame da jami'an rundunar suka gudanar a ranar Talata, 28 ga Yulin 2026.
Yadda aka kama wanda ake zargin
A cewar sanarwar, jami'an 'yan sanda na sashen Guma suna gudanar da binciken abubuwan hawa ne lokacin da suka tare wasu mutum biyu da ke tafiya a kan babur.
Da suka hango jami'an tsaro, ɗaya daga cikin mutanen ya sauko daga babur ya tsere zuwa cikin wani daji da ke kusa.
Sai dai jami'an sun samu nasarar cafke ɗayan mutumin mai suna Joro Jarkata, ɗan shekara 20 daga ƙaramar hukumar Awe ta jihar Nasarawa.
Tribune ta wallafa cewa binciken da aka yi masa ya sa aka gano alburusai 115 da ya ɓoye a cikin wata jaka da ya ke tare da ita.
'Yan sanda sun fara zurfafa bincike
Rundunar ta ce wanda ake zargin yana tsare a hannunta, yayin da aka miƙa shari'arsa zuwa sashen binciken manyan laifuffuka (SCID) da ke Makurdi domin ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan
'Ba Abuja ba ne,' 'Yan sanda sun gano jihar da 'yan ta'adda suka kashe babban soja
Ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke mutumin da ya tsere tare da gano inda aka samo alburusan da kuma inda ake shirin kai su.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Cletus Nwadiogbu, ya yabawa jami'an da suka gudanar da aikin bisa ƙwarewa da hanzarin da suka nuna.

Source: Twitter
Ya yi magana yana mai jaddada kudirin rundunar na dakile yaɗuwar makamai ba bisa ƙa'ida ba da kuma rusa hanyoyin da masu aikata laifi ke amfani da su.
An shirya shirya zanga-zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar Take It Back ta bukaci a sauke shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, kan takaddamar da ta shafi wata hukuma da aka ce ta bogi ce.
Mai kula da ƙungiyar na ƙasa, Juwon Sanyaolu, ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya su fito zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da aka shirya gudanarwa a ranar 5 ga Agustan 2026.
Ya ce zanga-zangar za ta mayar da hankali kan matsalolin tsaro, yunwa, tsadar rayuwa, tauye 'yancin dimokuraɗiyya da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Asali: Legit.ng
