2027: Dan Takarar Gwamnan APC Ya Saki Zantuttuka bayan Ganawa da Tinubu
- Sanata Aliyu Wadada ya ce akwai gagarumin ci gaba a tattalin arzikin Najeriya tun bayan hawar Bola Tinubu kan mulki
- Ya bayyana cewa bai dace a yi watsi da nasarorin gwamnatin ba, duk da cewa har yanzu akwai ƙalubalen da ke bukatar ƙarin aiki
- Sanatan ya gabatar da tsarinsa na HEARTS Agenda domin bunƙasa ilimi, lafiya, noma, ma’adanai da sauran fannoni a jihar Nasarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata Aliyu Wadada, mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, ya kare gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Wadada ya bayyana cewa sai “bayyanannen maƙiyin gwamnati” ne zai musanta nasarorin da ta samu.

Source: Twitter
Wadada ya yi wannan magana ne yayin da yake zantawa da wakilan fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a Fadar Aso Villa da ke Abuja a ranar Alhamis, 30 ga watan Yulin 2026, cewar rahoton jaridar Leadership.
Me Wadada ya ce kan gwamnatin Tinubu?
Sanatan ya ce alkaluman tattalin arziki sun nuna an samu gagarumin ci gaba tun bayan da Tinubu ya hau kan mulki.
Ya ce duk da cewa gwamnatin tana da sauran aiki a gabanta, ba zai zama abu mai ma’ana ba a yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba a muhimman bangarorin tattalin arziki.
“Amma duk wanda zai zauna ya yi fatan ganin wannan gwamnati ta gaza, to ko dai jahili ne, ko kuma ba ya kallon al’amura yadda suke, ko kuma bayyanannen maƙiyin gwamnati ne, domin adawa daban take da zama maƙiyi.” In ji shi
Wadada ya lissafo nasarorin Tinubu
Sanata Wadada ya ce an samu ci gaba a ma’aunin biyan bashin kasa da kasa, cinikayyar Najeriya da kasashen waje, ajiyar kudaden waje, daidaituwar farashin musayar kudade da kuma kasuwar hannayen jari.
Ya bayyana cewa wadannan abubuwa sun nuna sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau.
A cewarsa, ajiyar kudaden Najeriya na kasashen waje ta karu daga kasa da dala biliyan 30 lokacin da Tinubu ya hau mulki zuwa kusan dala biliyan 56 zuwa 57.
Ya kuma ce hada kasuwannin musayar kudaden waje wuri guda ya taimaka wajen kara daidaita darajar naira.

Source: Facebook
Sanatan ya kara da cewa ayyukan raya ababen more rayuwa da ake gudanarwa a fadin kasar nan, tare da bunkasar kasuwar hannayen jari, suna nuna ci gaban tattalin arziki a karkashin gwamnatin Tinubu.
Sai dai ya jaddada cewa nasarorin da aka samu ba sa nufin an warware dukkan matsalolin kasar.
“Akwai gagarumin ci gaba, sauye-sauye da bunkasa a kowane bangare, amma wannan ba yana nufin komai ya daidaita ba. Har yanzu akwai bukatar a kara yin aiki sosai.” In ji shi.
Tinubu ba zai biya kudin fansa ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta biya ’yan ta’adda kuɗin fansa ba.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a ɗauki matakan dabaru domin murƙushe masu aikata laifuffuka a faɗin Najeriya.
Asali: Legit.ng

