An Cimma Matsaya: Jami'ar ABU Za Ta Fara Koyar da Digirin Gudanar da Aikin Hajji
- Jami'ar Ahmadu Bello da NAHCON sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ƙaddamar da digirin MBA kan gudanar da harkokin Hajji da Umrah
- Shirin haɗin gwiwar zai haɗa da koyarwa, bincike, horaswa, ƙwarewar aiki da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa domin inganta harkokin gudanar da Hajji
- ABU za ta kula da harkokin ilimi da bayar da digiri, yayin da NAHCON za ta samar da ƙwararru, horaswa da gogewar gudanar da Hajji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kaduna - Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) ta ƙulla yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) domin haɗin gwiwa wajen ƙirƙiro da gudanar da shirin digirin MBA kan harkokin gudanar da Hajji.
An ƙulla yarjejeniyar ne ta Cibiyar Koyon Nesa ta ABU da Cibiyar Nazarin Hajji ta Najeriya, da ke ƙarƙashin NAHCON.

Source: UGC
Yarjejeniyar MBA kan Hajji a ABU Zaria
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a wani taƙaitaccen biki da aka gudanar a Hajj House da ke Abuja ranar Juma'a, 31 ga Yulin 2026, kamar yadda aka wallafa a shafin ABU na intanet.
Babbar manufar yarjejeniyar ita ce samar da tsarin haɗin gwiwa wajen tsarawa, gudanarwa da ci gaba da inganta harkokin gudanar da Hajji.
Yarjejeniyar ta haɗa da haɗin gwiwa wajen tsara manhajar karatu da duba ta lokaci-lokaci, tare da koyar da kwasa-kwasai na musamman kan Hajji da Umrah.
Haka kuma, za a gudanar da tarukan ƙwararru, horas da manyan jami'ai, ba ɗalibai damar yin aikin ƙwarewa, gudanar da bincike da ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomi da cibiyoyin ƙasa da ƙasa.
Rawar da ABU za ta taka
Bisa yarjejeniyar, Jami'ar Ahmadu Bello za ta kula da dukkan harkokin ilimi na shirin ta hannun Cibiyar Koyon Nesa.
Haka kuma, jami'ar za ta tabbatar da samun dukkan amincewa da takardun shaidar da ake buƙata domin gudanar da shirin.
ABU za ta karɓi ɗaliban da suka cika sharudda bisa ƙa'idodin jami'ar, ta samar da malamai masu koyar da darussan gudanarwa da makamantansu.
Har ila yau, jami'ar ce za ta shirya jarabawa, tantance sakamako tare da bayar da digirin MBA a fannin gudanar da harkokin Hajji.
Za ta kuma kula da harkokin gudanarwa da tallafa wa ɗalibai, tare da tabbatar da bin ƙa'idojin ingancin ilimi na jami'ar.
Ayyukan da NAHCON za ta gudanar
A nata ɓangaren, NAHCON za ta samar da jagoranci na fasaha kan harkokin Hajji da Umrah ta hannun Cibiyar Nazarin Hajji ta Najeriya.
Hukumar za ta zaɓo ƙwararrun masu aiki a fannin a matsayin malamai na wucin gadi da masu ba da horo, bisa sharuddan da jami'ar ta gindaya.
Haka kuma, za ta taimaka wajen samar da guraben koyon aiki da ziyartar cibiyoyin gudanar da Hajji a Najeriya da ƙasashen waje.

Source: UGC
An kare haƙƙin bincike da mallakar ilimi
Bangarorin biyu sun amince da muhimmancin adanawa da yaɗa sakamakon binciken da za a gudanar a ƙarƙashin wannan shiri.
Sun kuma bayyana cewa yarjejeniyar ba za ta shafi haƙƙin mallakar ilimi ko marubucin bincike da ya rataya a wuyan ɗalibai da jami'ar ba.
Asali: Legit.ng


