Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 102, An Cafke 345

Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 102, An Cafke 345

  • Hedikwatar Tsaro ta ce dakarun Najeriya sun kashe sama da 'yan ta'adda da masu laifi 102 tare da cafke mutum 345 a watan Yulin 2026
  • Sojojin sun ceto mutane 393 da aka sace, sun kwato makamai 59 da harsasai 1,118, yayin da 'yan tawaye 57 suka miƙa wuya
  • Dakarun Operation Delta Safe sun lalata wuraren tace mai ba bisa ka'ida ba 18 tare da kwato sama da lita 250,500 na kayayyakin man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abuja - Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun rundunar sojin ƙasar sun kashe sama da ’yan ta’adda da masu aikata laifuka 102 a sassa daban-daban na ƙasar cikin watan Yulin 2026.

Daraktan Yaɗa Labarai na Ayyukan Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin taron bayanin ayyukan tsaro na wata-wata.

Kara karanta wannan

Manyan sauye sauye 6 da aka kawo a gasar Premeir League a kakar wasa ta 2026/27

Sojojin Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda 102 a cikin kwanaki 30
Sojojin Najeriya da ke yaki da 'yan ta'adda a dazuzzukan Najeriya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

An kashe 'yan ta'adda an kama wasu

Ya ce baya ga kashe ’yan ta’addan, dakarun sun kama mutum 345 da ake zargi da hannu a ta’addanci da sauran laifuka, sun kuma ceto mutane 393 da aka yi garkuwa da su, in ji rahoton Arise News.

Onoja ya ƙara da cewa an kwato bindigogi 59 da harsasai 1,118, yayin da ’yan tada kayar baya 57 suka mika wuya ga jami’an tsaro a cikin wannan lokaci.

Ayyukan da aka gudanar a yankuna

A yankin Arewa maso Gabas, dakaru sun kashe mayaƙa 54, sun kama ’yan ta’adda 102, sannan suka ceto mutane 102 da aka sace. Haka kuma, ’yan tada kayar baya 57 tare da iyalansu sun mika wuya.

A Arewa maso Yamma, rundunar Operation Fansan Yamma ta kashe mayaƙa 33, ta kama mutum 66 da ake zargi da ta’addanci, sannan ta ceto mutane 191 daga hannun masu garkuwa.

Kara karanta wannan

'Fulani ba 'yan ta'adda ba ne,' Sarkin Musulmi ya yi magana kan matsalar tsaro

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, dakaru sun kashe ’yan ta’adda 15, sun kama mutum 148, tare da ceto mutane 53.

A yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, an ceto mutane 47, yayin da aka kama mutum 29 da ake zargi da aikata laifuka.

Sojjin Najeriya sun kai hare-hare da dama inda suka kakkabe 'yan ta'adda 107
Sojojin Najeriya suna tafiya a kan tankar yaki. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

An lalata matatun mai ba bisa ka’ida ba

DHQ ta kuma ce rundunar Operation Delta Safe ta ci gaba da gudanar da farmaki kan masu satar danyen mai a jihohin Akwa Ibom, Edo da Rivers.

A cewar Onoja, dakarun sun lalata matatun mai ba bisa ka’ida ba guda 18, tare da kwato fiye da lita 250,500 na danyen mai da man fetur da aka tace ba bisa ka’ida ba.

Ya ce a wasu hare-hare da aka kai a yankunan Ahoada West, Ahoada East da Okrika na jihar Rivers, an gano sansanonin satar mai da dama, inda aka kwato dubban lita na danyen mai da man fetur kafin a lalata wuraren.

Sojoji sun gwabza da 'yan bindiga

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun Operation Fansan Yamma sun yi artabu da mayaƙan Ado Allero inda aka dauki tsawon lokaci ana dauki ba dade a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta ana tsaka da garkuwa da mutane a hanyar Kano

Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauki lokaci ana musayar wuta, lamarin da ya jawo mutuwar wasu da yawa yayin da wasu su ka samu raunuka.

Sojoji su na ci gaba da akin farautar fitinannun yan ta'addan da su ka addabi jama'a yayin da ake dakon wasu muhimman bayanai daga rundunar sojin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com