'Yan Daba Sun Afka Dakin Kwanan Dalibai Mata na ATBU, an Yi Barna Mai Girma

'Yan Daba Sun Afka Dakin Kwanan Dalibai Mata na ATBU, an Yi Barna Mai Girma

  • Wasu 'yan daba dauke da makamai sun kutsa dakunan kwanan dalibai mata na Jami'ar ATBU da ke Gubi a jihar Bauchi
  • Maharan sun yi wa dalibai mata fashi tare da raunata wasu, inda suka kwashe sama da wayoyi 50 da sauran kayayyaki masu daraja
  • Hukumar jami'ar ta tabbatar da faruwar lamarin, yayin da 'yan sanda suka fara bincike kan lamarin mara dadin ji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Wasu 'yan daba dauke da makamai sun kai farmaki dakunan kwanan dalibai mata na Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), harabar Gubi da ke jihar Bauchi.

'Yan daban sun kwashe wayoyin hannu da sauran kayayyaki masu daraja yayin farmakin da suka kai a jami'ar ATBU.

Yan daba sun kai hari a ATBU
Kofar shiga jami'ar ATBU da ke Bauchi Hoto: ATBU Updates
Source: UGC

Wata shaidar gani da ido da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru da misalin karfe 2:00 na dare a ranar Litinin, 27 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta ana tsaka da garkuwa da mutane a hanyar Kano

Ta ce maharan sun zo dauke da adduna, wukake da sauran makamai masu hadari, yayin farmakin da suka kawo.

Maharan sun shiga dakuna fiye da 10

A cewar shaidar, 'yan daban sun kutsa cikin dakuna fiye da 10, inda suka razana dalibai tare da kwashe sama da wayoyin hannu 50 da sauran kayayyaki masu daraja.

Ta kara da cewa wasu daga cikin daliban sun samu raunuka yayin harin.

"Sun jikkata wasu daga cikin wadanda abin ya shafa. Wata daliba ta samu munanan raunuka bayan ta ki mika wayarta," in ji ta.

Shaidar ta bayyana cewa lamarin ya kara jefa dalibai cikin fargaba kan tsaro a harabar Gubi, tana mai cewa jami'ar na makwabtaka da wasu kauyuka da kuma dazuzzuka masu yawa.

Hukumar jami'a ta tabbatar da harin

Da aka tuntubi daraktan yaɗa labarai da hulda da jama'a na jami'ar, Zailani Bappa, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce shugaban jami'ar, Farfesa Ibrahim Hassan Garba, ya kai ziyara dakunan kwanan daliban domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu da kudirin hukumar jami'ar na inganta tsaronsu.

Kara karanta wannan

Yan sandan MOPOL sun nemi agajin Sufeton Ƴan sanda watanni 7 da hana su alawus

Bappa ya ce jami'ar ta dauki matakan gaggawa tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin kara tsaurara matakan tsaro a harabar makarantar, tashar Channels tv ta kawo labarin.

"Lamarin an kai rahotonsa ga 'yan sanda. Sun tura jami'ansu zuwa harabar jami'ar, sun karbi bayanan wadanda abin ya shafa, kuma sun fara gudanar da bincike," in ji shi.
'Yan daba sun yi ta'asa a ATBU
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dalibai sun bukaci a kara tsaro

Tun bayan faruwar lamarin, ana ci gaba da tattaunawa a cikin al'ummar jami'ar da kuma shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke kira da a kara inganta tsaro a yankin dakunan kwanan dalibai tare da kamo wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kotu.

Wasu daliban sun kuma bukaci mahukuntan jami'ar su taimaka wajen maye gurbin kayayyakin da aka sace, tare da kara yawan jami'an tsaro a harabar Gubi da ke bayan garin Bauchi.

Farfesa Yelwa ya ajiye limanci a ATBU

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban limamin masallacin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ce ya ajiye limanci.

Babban malamin musuluncin ya ce ya fahimci ajiye limancin ne ya fi dacewa idan har makarantar bata sauya matsaya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng