Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojan sama sun tarwatsa mafakar Boko Haram, sun kashe da dama

Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojan sama sun tarwatsa mafakar Boko Haram, sun kashe da dama

Dakarun rundunar Sojan saman Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen ragargazan mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a wani samame da suka kai musu yayin da suka taru a sansanoninsu a yankin tafkin Chadi.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito jiragen yakin Sojojin sun yi ma kungiyar watsa watsa ne a sansanoninsu dake yankin Arinna Ciki a kusa tafkn Chadi, Arewacin jahar Borno, kamar yadda kaakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola.

KU KARANTA: Ikon Allah: An gano wani yaro Anambra da inyamurai a suka saceshi daga Kano a 2014

Daramola ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, inda yace dakarun Sojan sama na Operation Lafiya Dole sun halaka wasu mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP Boko Haram a yayin ruwan wuta da suka yi musu.

“Mun samu wannan nasara ne a wasu hare hare da muka kaddamar a sansanonin Boko Haram a ranakun 1 da 2 na watan Nuwamba bayan samun bayanan sirri dake tabbatar da tattaruwar yan ta’adda a sansanin domin shirya yadda zasu kai ma Sojoji hari.

“Mun kai harin farko ne bayan na’urar leken asirinmu ta gano wasu motocin mayakan ISWAP a karkashin wasu bishiyoyi a yankin, nan da nan muka aika jiragen yakinmu suka dagargaza sansanin tare da motocin duka.

“Hari na biyu kuwa mun kaddamar da shi ne bayan mun gano wasu yan ta’adda suna ta hada hada a wani yanki na daban, daga nan muka sake aika jiragenmu na yaki, inda suka lalata sansanin tare da halaka duka yan ta’addan dake wurin.” Inji shi.

Daga karshe Daramola ya bayyana cewa zasu cigaba da kokarin kakkabe ragowar mayakan Boko Haram daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya tare da hadin gwiwar sojojin kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel