Za mu kammala ginin sabuwar titi daga Abuja zuwa kasar Algeria cikin shekaru 3 – Fashola

Za mu kammala ginin sabuwar titi daga Abuja zuwa kasar Algeria cikin shekaru 3 – Fashola

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kammala aikin titin daya tashi daga Abuja zuwa birnin Algiers na kasar Algeria.

Fashola ya bayyana haka ne yayin ziyarar gani da ido daya kai wani sashi na aikin a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, inda yace gwamnati za ta kammala aikin ne cikin shekaru 3 masu zuwa.

KU KARANTA: Ikon Allah: An gano wani yaro Anambra da inyamurai a suka saceshi daga Kano a 2014

A ziyarar gani da ido daya kai, Fashola ya leka sashin Abuja-Keffi-Akwanga-Lafia-Makurdi da kuma aikin titin Abuja-Kaduna. Ziyarar na daga cikin ayyukan da aka ware domin taron kwanaki biyu na kwamitin gina sabuwar hanya daga Abuja zuwa Algeria, karo na 70 da aka fara tun a ranar 11 ga watan Nuwamba.

“Abinda kwamitin ya fi damuwa da shi, shi ne aikin titin Legas zuwa Algiers, Legas-Ibadan-Oyo- da Jebba-Mokwa-Kaduna-Kano da Abuja-Kano su ne manyan hanyoyin, don haka Mali na yin nata, Algeria ma haka, Nijar ma haka.

“Hanyar Abuja zuwa Kaduna tagwayen tituna ne dake da tsawon kilomita 375.9 kuma yana da sassa guda uku, sa’annan zamu kammala shi cikin shekaru uku.” Inji shi.

Fashola ya kara da cewa sashin da gwamnati ta bayar da aikinsa ga kamfanin China Harbur Engineering Company Limited shi ne aikin fadada titin Abuja zuwa Keffi tsawon kilomita 5.4 da kuma mayar da hanyar keffi zuwa Akwanga tagwayen tituna.

Ministan ya cigaba da fadin baya ga gina tituna, za’a samar da gadoji da kwalbatoci da kuma hanyoyin matafiyan kasa. A yayin zagayen, sakataren kwamiyin aikin titin Najeriya zuwa Algeria, Ayadi Muhammad ya bayyana cewa sun ziyarar ta basu daman gane ma idanunsu matakin aikin da ake yi.

Ayadi ya yaba da ayyukan da ya gane ma idanunsa gwamnatin Najeriya na yi. Idan aka kammala wannan aiki, ana sa ran hanyar za ta hada yankunan Afirka guda 37, manyan birane 74 da akalla mutane miliyan 60 daga kasashen Afirka guda 6.

A Najeriya kawai, titin zai ratsa jahohin Legas, Ibadan, Ilorin, Jeba, Kaduna zuwa Kano inda Najeriya ta yi iyaka da kasar Nijar. Kasashen da suka dauki nauyin wannan aiki sun hada da Najeriya, Algeria, Nijar, Mali, Chad da Tunisia.

Tun a shekarar 1966 aka kafa wannan kwamiti domin ta samar da hanyar data hada kasashen 6 don karfafa cigaban tattalin arziki da kuma kawancen cinikayya tsakanin kasashen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel