Duk da Rashin Tabbas Kan Makomarta, Tsagin PDP Ya Mika Sunan Jonathan ga INEC

Duk da Rashin Tabbas Kan Makomarta, Tsagin PDP Ya Mika Sunan Jonathan ga INEC

  • Tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki ya ce ya miƙa wa INEC takarar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan
  • Tsagin ya ce ya bi tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 wajen miƙa sunayen da hannu, tare da gargaɗin INEC kada ta wallafa wata dabam
  • PDP ta zargi INEC da nuna son kai, tana mai cewa za ta bi duk hanyoyin shari'a domin kare jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsagin PDP ƙarƙashin Kwamitin Riƙon Ƙwarya na Ƙasa da Kabiru Turaki ke jagoranta ya tura sunan dan takarar jam'iyyar ga INEC.

Tsagin ya bayyana cewa ya miƙa wa INEC takarar tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da sauran 'yan takararsa.

Tsagin PDP ya mika wa INEC sunan Jonathan
Goodluck Jonathan wanda tsagin PDP ta tsayar a matsayin dan takarar shugaban kasa. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

An mika sunan Jonathan ga INEC

Kwamitin ya ce ya miƙa sunayen da hannu bayan INEC ta ƙi ba shi lambobin shiga domin miƙa takardu ta shafin hukumar, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 7 sun shirya yaki domin tabbatar da nasarar Tinubu a 2027

Sakataren yaɗa labarai na kwamitin, Ini Ememobong, ya shaida wa manema labarai cewa sun cika dukkan sharuddan doka wajen gabatar da sunayen 'yan takarar jam'iyyar.

Ya ce jerin sunayen da aka miƙa sun haɗa da takarar shugaban ƙasa ta Goodluck Jonathan, da 'yan takarar gwamnoni, Majalisar Tarayya da majalisun dokokin jihohi.

Ememobong ya yi gargaɗi cewa idan hukumar INEC ta wallafa sunayen da ba waɗanda suka miƙa ba, za su bi dukkan hanyoyin kundin tsarin mulki da na shari'a domin kare haƙƙinsu.

Ya ce rikicin ya samo asali ne bayan hukuncin Kotun Koli kan shugabancin PDP, wanda ya bar jam'iyyar ba tare da shugabancin ƙasa da aka amince da shi ba, cewar Daily Post.

Tsagin PDP karkashin Turaki ya yi zarge-zarge kan INEC
Shugaban tsagin PDP, Kabiru Tanimu Turaki. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Source: Twitter

Rokon tsagin PDP ga Kotun Tarayya

A cewarsa, kwamitin amintattu da taron kwamitin zartarwa na ƙasa ne suka kafa Kwamitin Riƙon Ƙwarya, amma INEC ta ƙi amincewa da shi duk da sanarwar da aka aika mata.

Kara karanta wannan

An kafawa Tinubu sharuda 9 yayin da za a yi zanga zangar kasa baki daya

Ya kuma soki hukuncin Babbar Kotun Tarayya, yana cewa ya saɓa da hukuncin Kotun Koli da Kotun Ɗaukaka Ƙara, saboda haka sun ɗaukaka ƙara tare da ƙalubalantar wasu bayanai da ke cikin kwafin hukuncin.

PDP ta kuma zargi INEC da rashin nuna tsaka-tsaki, tana mai cewa wasu matakan da hukumar ke ɗauka na rage amincewar jama'a da tsarin zaɓe tare da raunana jam'iyyun adawa.

Ememobong ya yi kira ga 'yan Najeriya su kare tsarin dimokuraɗiyyar jam'iyyu masu yawa, yana mai cewa jam'iyyar na da tabbacin za ta yi nasara ta hanyar doka.

An tura sunan Pantami a shafin INEC

An ji cewa kungiyar Pantamiyya Movement ta sanar da cewa jam'iyyar PDP ta kammala tura bayanan takarar Farfesa Isa Ali Pantami zuwa shafin hukumar INEC.

Kungiyar ta ce an sanya bayanan Pantami a ranar 26 ga Yulin 2026 bayan ya zama dan takarar gwamna ba tare da hamayya ba a zaben fitar da gwani.

Pantamiyya ta bayyana cewa hakan wata muhimmiyar nasara ce ga dimokuradiyya, tana mai nuna kwarin gwiwar samun shugabanci nagari a Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.