Ina jin mutuwa zanyi - 'Yar aiki a kasar Saudiyya ta bayyana yadda ubangidanta yake cin zarafinta a wani bidiyo

Ina jin mutuwa zanyi - 'Yar aiki a kasar Saudiyya ta bayyana yadda ubangidanta yake cin zarafinta a wani bidiyo

- Wata mata 'yar kasar Bangladesh mai aiki a kasar Saudi Arabia ta saki wani bidiyo inda take neman tallafi a tseratar da rayuwarta

- Ta bayyana yadda ubangidanta ya ci zarafinta tare da kona da tafasasshen mai inda daga bisani ya daureta tare da kulleta a daki

- Matar ta bayyana cewa, tayi kwanaki 15 a dakin inda da kyar suke bata abinci

Wata mata 'yar kasar Bangladesh mai yin aiki a wani gida a kasar Saudi Arabia ta fitar da wani faifan bidiyo mai cike da al'ajabi inda take bukatar taimako. A bidiyon ta zargi ubangidanta da cin zarafinta kuma ta bukaci tallafin jama'a don ceto rayuwarta.

Matar ta fitar da faifan bidiyon ne a sirrance kuma tana zubda hawaye akan cin zarafinta da ake yi, ta bayyana yadda aka konata da man gyada mai zafi sannan aka daureta. Matar dai ta bayyana cewa yanzu babban burinta shine koma gida Bangladesh amma an rufeta na sama da makonni biyu.

Matar mai shekaru 25 tace: "Akwai yiwuwar kwana ne ya zo karshe, ku taimake ni sun garkameni a daki ne na kwanaki 15, da kyar suke bani abinci, sun kona min hannaye da mai kuma sun daure ni."

"Suna daukata daga wannan gida zuwa wani inda suke azabtar dani tare da dukana, ban tunanin zan rayu, ina tunanin mutuwa zanyi. Ku taimakeni ku tseratar dani."

Kamar yadda wata kungiyar taimakon kai da kai mai suna BRAC ta Bangladesh din ta sanar, an kwace wayar hadimar a gidan sakamakon bidiyon da ta saki.

KU KARANTA: Na fi kaunar mijina idan yana talauci - Wata mata ta bayyana sirrinta

A halin yanzu tana rayuwa a Jeddah. Hukumomi daga kasar ta sun yi kira sannan kuma anyi zanga-zanga a babban birnin Bangaladesh din, Dhaka.

Mai magana da yawun gwamnatin, Atiqur Rahman yace dole ne a rufe cibiyoyin samar da ire-iren wannan aiyukan.

Amma kuma ministan harkokin waje, AK Abdul yace ba zasu hana mata zuwa Saudiyya aiki ba.

Ya ce: "Kasar Saudiyya ta sani sarai ana azabtar da mutane, amma kalilan ne hakan ke faruwa dasu, ba gwamnatin Saudiyya bace take azabtar dasu."

A watan da ya gabata, an samu gawar wata mata mai suna Nazma Begum bayan da ta dinga kiran danta da bukatar ya ceceta. Tsananin azabtarwa ce ta sa Begum mai shekaru 42 ta rasu sakamakon cutar da ta kwantar da ita.

Kungiyar BRAC da ke Dhaka tace, a wannan shekarar kadai, an samu gawawwaki 48 na mata da ke aiki a Saudiyya da aka dawo dasu zuwa Bangladesh.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel