Jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Stanley Osifo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027. Zai fafata da Shugaba Bola Tinubu.
Jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Stanley Osifo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027. Zai fafata da Shugaba Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya yi gargadi kan shirin hana kamfen din 2027 a jihohin Arewa takwas da suka hada da Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi, Kano.
Babban sakataren labarai na jam’iyyar, Yekini Nabena wanda ya saki jerin sunayen a wata sanarwa yace sakamakon ya kasance na ganawar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba.
Mun ji labari cewa ana nema ayi bore a Mahaifar Shugaban kasa na tsaida ‘Dan uwan Buhari takara. Yanzu haka APC na neman kakaba wani ‘Dan uwan Buhari a matsayin ‘Dan Majalisan Daura da da Mai’Adua da kuma Sandamu.
Mun ji cewa zaben tsaida ‘Yan takarar APC ya bar baya da kura a wasu Jihohi inda wasu ‘Yan takara sun rubutawa Shugaban Jam’iyyar APC wasika a sake zabe. Daga ciki akwai Prince Ikonne wanda yace da su aka kafa APC.
Rikici ya barke a Jam’iyyar APC a dalilin zaben tsaida ‘Dan takara. Jama’a sun yi zanga-zanga na neman hana David Umaru takara. Zanga-zanga ne ya barke bayan Sanatocin Jihar Neja sun fadi zabe duk da su na kan mulki.
Kwamishinan Ilimi na jihar Gombe, Hajiya Aishatu MB Ahmad ta kayar da kawunta, Samaila Mu'azu Hassan, wanda shine dan majalisa mai wakiltan mazabar Akko a majalisar wakilai na tarayya a zaben fidda gwani na PDP a jihar Gombe.
Wani dan majalisar wakilai da ya shafe zango uku a majalisar, Isa Bashir-Kalanjeni ya sake samun tikitin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) takarar kujerar mazabar Tangaza/Gudu a jihar Sokoto a zaben 2019.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan man fetur, Sanata Kabiru Garba Marafa ya goyi bayan hukuncin soke zaben fidda gwani na gwamna da kwamitin jam’iyyar APC tayi jiya a jihar Zamfara, duk da cewar shi ne ke kan gaba a zaben.
Mun samu labari kai tsaye daga Kano cewa wani ‘Dan Majalisar Tarayyar Kano da ke kan kujera ya sha kasa a zaben kato bayan kato. Hafiz Kawu ya tika ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Tarauni a Majalisa watau Honarabul Nasiru Babale Ila
Yayinda sanatoci uku daga jihar Niger suka rasa kudirinsu na yin tazarce inda sabbin shiga suka lashe zaben fidda gwani na samun tikin jam’iyyar APC, sanatocin sun dauki zafi inda suka yi zargin cewa anyi murdiya a zaben.
Siyasa
Samu kari