Jama’a sun yi zanga-zanga na neman hana David Umaru takara
Mun samu labari cewa rikici ya barke a Gabashin Jihar Neje bayan zaben fitar da gwani da Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar da ma kasa baki daya ta fitar inda Sanatan da ke wakiltar Yankin ya sha kasa.

Asali: Depositphotos
Jama’a sun fito sun nuna rashin jin dadin su da sakamakon zaben da APC ta shirya na Sanatoci inda Sanata David Umaru ya fadi war-was. Hakan ya sa mutane su ka cika gidan su su na masu zanga-zanga domin nuna rashin jituwa.
Masu zanga-zangar sun nuna cewa an nuna son-kai wajen zaben na tsaida ‘Yan takara. Har wa yau, masu zanga-zangar sun fito su na cewa idan har babu Sanata Umaru to lallai babu Jam’iyyar APC mai mulki a gaba daya Jihar Neja.
KU KARANTA: Wasu Gwamnoni za su yi takarar kujerar Sanata a Jam’iyyar APC
Har yanzu dai ba a sanar da sakamakon zaben ba amma da alamu Sanatan da ke kan kujera Umaru zai rasa kujerar sa wajen Musa Sani. Ana dai kukan ba ayi zabe ba sam a Yankin don haka Uwar Jam’iyya ta shiya sabon zabe a yau.
Mutanen Yankin dai sun nuna shakka babu su na tare da Baba Buhari da kuma David Umaru inda su ka nemi APC ta sake duban lamarin. Wani Hadimin Sanatan dai ya nemi Jama’a su guji kawo abin da zai tada rikici a Yankin Jihar.
Jiya kun samu labari cewa Sanata Umaru Ibrahim Kurfi wanda ke wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar Dattawa ya fadi zaben fitar da gwani inda ya zo na hudu a zaben da aka shirya a Jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng