Rikicin siyasar Zamfara ya hada Oshiomhole da mataimakinsa rigima

Rikicin siyasar Zamfara ya hada Oshiomhole da mataimakinsa rigima

- A Zamfara, har kisan kai aka yi saboda zafin siyasa

- Uwar Jam'iyya ta kasa bata yarda da dorin da Yari ke neman yi ba

- Mataimakin Adams Oshiomhole ya ki amincewa da umarnin oga

Rikicin siyasar Zamfara ya hada Oshiomhole da mataimakinsa rigima
Rikicin siyasar Zamfara ya hada Oshiomhole da mataimakinsa rigima
Asali: UGC

Bayan da aka ki amincewa da yadda zabukan cikin gida na 'yan takara ke gudana a Zamfara, inda har asarar rayuka aka samu a bangarorin jam'iyyar ta APC, uwar jam'iyya ta rushe gabadayan shuwagabannin jam'iyyyar na jihar.

Sai dai, Mataimakin shugaban APC a yankin Arewa maso yamma, LAwal Shuaibu, yace sam hakan bai dace ba, ace wai an sauke shuwagabanni ana tsaka da zabe.

Ya kuma qara da cewa, wadanda aka sauke din, basu sauku ba, labaran na bogi ne, tunda batun yana gaban kotu.

DUBA WANNAN: An gano ashe Osama bin Laden ne ya taimaki Boko Haram

Ana cikin wannan ja'inja dai a yau, kuma za'a gudanar da babban taro na kasa na APC, dama na PDP, ita kuwa INEC, tace Allankatafar baza da qara wa jam'iyyu koda awa daya ba daga gobe lahadi, don haka, duk wanda bai kawo sunan dan takara ba, babu shi a zaben na 2019.

Yanzu dai, masu neman takara sunyi carko carko, yayin da manyan jam'iyyar kuma hankalinsu ya koma babban taro na kasa, ko ya zata qarke? Maji!

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewanku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng