Gwamnan Legas Ya Bi Sahu, Ya Nuna Wanda Yake Goyon Bayan Ya Gaje Shi a Zaben 2027

Gwamnan Legas Ya Bi Sahu, Ya Nuna Wanda Yake Goyon Bayan Ya Gaje Shi a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ayyana goyon bayansa ga mataimakin gwamna, Dr. Obafemi Hamzat don ya zama magajinsa a 2027
  • Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a wani taron jiga-jigan APC da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Legas yau Litinin
  • Gwamnan ya lara da cewa Hamzat na da kwarewa da ilimi mai zurfi da zai ba shi damar jagorantar jihar Legas yadda ya kamata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihag Lagos, Nigeria - Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana goyon bayansa ga mataimakinsa, Dr. Obafemi Hamzat, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2027.

Gwamna Sanwo-Olu ya furta haka ne yayin da tawagar mataimakin gwamnan ta kai masa ziyara a wani bangare na neman shawarwari kafin Hamzat ya ayyana fitowa takara a hukumance.

Hamzat.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu tare da mataimakinsa, Kadri Hamzat a taron Majalisar zartarw ata Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce wannan taron ya samu halartar mambobin Majalisar zartarwa ta jiha da shugabannin jam'iyyar APC na jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri zai fafata da babban dan kasuwa kan kujerar sanata a zaben 2027

Haka kuma, shugabannin kananan hukumomi da na yankunan ci gaban kananan hukumomi 57 da ake da su a jihar Legas duk sun halarci zaman.

A kwanakin baya dai an yada jita-jitar cewa dan shugaban kasa, Seyi Tinubu na iya neman kujerar gwamnan Legas a babban zabe mai zuwa.

Gwamnan Legas ya zabi magajinsa

Amma a taron da ya gudana yau Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2027, Gwamna Sanwo-Olu ya zabi mataimakinsa a matsayin wanda yake goyon bayan ya zama magajinsa.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa yin aiki tare da Hamzat a cikin shekaru bakwai da suka gabata ya nuna masa cewa shi mutum ne mai “tsatstsar gaskiya, biyayya, sadaukarwa, da kuma goyon baya”.

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, wanda Imran Muhammad ya wallafa a shafin X, an ga Sanwo-Olu ya daga hannun Hamzat, bayan ya yi masa addu’a, yayin da wadanda ke wurin ke tafi da murna.

Dalilin goyon bayan takarar Kadri Hamzat

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Gwamna Sanwo-Olu ya ce amincewa da takarar tasa matsaya ce ta bai-daya da masu ruwa da tsaki suka yanke.

Kara karanta wannan

Rurum ya samu goyon baya domin maye gurbin Kawu Sumaila a Majalisar Dattawa

“Mun karbi bakuncin Mataimakin Gwamna, wanda ya zo tare da wata tawaga mai karfi ta shugabanninmu a jihar nan domin sanar da mu aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamnan Legas.
“Dukanmu mun amince da cewa shi mutum ne da ya dace kuma ya shirya tsaf domin wannan aiki. Shi mutum ne da ya san ko’ina a cikin gidan nan."
“Muna godiya ga ubanmu, shugabanmu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya yi wannan hangen nesa, hangenda shi ne abin da ya fara bayyana a nan yau."

- Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Gwamnan Legas.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu lokacin da ya daga hannun mataimakinsa, Obafemi Hamzat domin nuna goyon baya Hoto: Dr. Obafemi Hamzat
Source: Facebook

Gwamna Sule ya zabi magajinsa a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ayyana Sanata Ahmed Wadada a matsayin wanda yake so ya gaje shi a zaɓen 2027.

Gwamna Sule ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa ta tsawon shekara guda da aka gudanar da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen jihar.

Ya jaddada cewa an bi matakai daban-daban kafin a tsame Sanata Wadada daga cikin mutane uku da aka tantance a matakin ƙarshe na wannan bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262