Babbar Magana: Zaben Shugaban Kasar Najeriya Zai Yi Zafi kamar Yaki a 2027
- Jigo a jam'iyyar adawa ta ADC, Dele Momodu ya kwatanta zaben shugaban kasa da yaki saboda yadda ake fafatawa wajen neman nasara
- Momodu, wanda fitaccen dan jarida ne ya bukaci matasan Najeriya su farka daga barci, su shiga harkokin siyasa gadan-gadan
- Ya kuma bayyana cewa ya gamsu da tafiyar da yake kai ta siyasa, wanda hakan ya sa bai shiga jam'iyyar APC ba duk da kusancinsa da Bola Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun, Nigeria - Fitaccen ɗan jarida kuma mawallafin Mujallar Ovation, Dele Momodu, ya buƙaci matasan Najeriya su ƙara zage damtse wajen shiga harkokin siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Ya bayyana cewa lokaci ya yi da matasa za su daina tsaya wa kan surutun baka ko rubutun soshiyal midiya, su koma yin aiki a aikace domin samun tasiri a siyasa.

Kara karanta wannan
Gwamna zulum ya fadi manyan dabaru 2 da ke ba ƴan ta'adda damar kai wa sojoji hari

Source: Facebook
Yadda ake yaki a zaben shugaban kasa
Jaridar Punch ta ce Momodu, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun, yayin wani taron karatu na “Reading Time”
Ya ce siyasa musamman zaɓen shugaban ƙasa yana yin zafi zafi matuka musamman a wannan karo, har ya kwatanta shi da yaƙi.
“A lokacin da na tsaya takara a 2011, na gane cewa siyasa ba wasa ba ce. Zaɓen shugaban ƙasa kamar yaƙi ne musamman a wannan karon, domin ana fafatawa ne kan nasara ɗaya tilo,” in ji shi
Dalilin Dele Momodu na kin shiga APC
Momodu ya kuma bayyana cewa bai shiga jam’iyyar APC ba duk da kusancinsa da shugaban kasa Bola Tinubu, saboda ya gamsu da tafarkin da yake kai a yanzu.
Ya kara da cewa da don kudi yake siyasa, da tuni ya sauya aheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, kamar yadda Daily Post ta ruwaito shi yana fada.
“Idan da kuɗi ne burina, da tuni na shiga APC. Na yi aiki tare da shugaban ƙasa a baya, amma na zaɓi in tsaya kan gaskiya,” in ji shi.
Momodu ya tuna rayuwarsa a jami'ar OAU
Jigon na ADC ya tuna da rayuwarsa a jami’ar OAU, inda ya ce ya koyi darasin wadatar zuci duk da talaucin iyayensa.
A cewarsa, iyayensa sun yi iya ƙoƙarinsu wajen tura shi makaranta, lamarin da ya taimaka masa a rayuwa.

Source: Facebook
Wannan kalamai da Dele Momodu na zuwa ne yayin da jam'iyyar hadaka ta ADC ke ci gaba da shirye-shiryen kalubalantar Shugaba Tinubu da APC a babban zaben 2027.
APC ta samu mukami a Majalisar Dattawa
A wani rahoton, kun ji cewa ADC ta fara samun kujerun shugabanci a Majalisar dattawa ta 10 bayan sauya shekar wasu sanatoci a Najeriya.
Majalisar dattawan Najeriya ta nada Sanata Tony Nwoye na jam’iyyar ADC a matsayin sabon mai tsawatarwa na marasa rinjaye.
Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ADC ta zama babbar jam’iyyar adawa a majalisar dattawa, inda take da sanatoci tara, yayin da PDP ke da guda biyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
