Shugaba Tinubu Ya Samu Wanda Za Su Fafata wajen Neman Tikitin APC a Zaben 2027
- Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu wanda za su fafata wajen neman tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC
- Stanley Osifo ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2027
- Ya bayyana cewa zai gwada sa'arsa duk kuwa da irin goyon bayan da gwamnonin APC suka ba Shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Stanley Osifo ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar neman tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027.
Bayyana aniyar Stanley Osifo ta nuna cewa zai ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu duk da jerin goyon bayan da shugaban kasar mai ci yake samu.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Stanley Osifo ya bayyana aniyarsa ne a ranar Litinin, 27 ga watan Afirilun 2026 yayin wani taron manema labarai a Abuja.
Stanley Osifo zai nemi tikitin APC
Stanley Osifo ya sanar da shirinsa na sayen fom ɗin tsayawa takara na jam’iyyar APC kan kuɗi Naira miliyan 100 gabanin gudanar da zaɓen fitar da gwani.
Wannan sanarwa tasa tana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun haɗin kai a cikin jam’iyya mai mulki, inda dukkan gwamnonin APC su 22 suka amince da Tinubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Shin Tinubu ke daukar nauyinsa?
Yayin da yake mayar da martani kan jita-jitar da ake yi game da waɗanda ke mara masa baya, Osifo ya yi watsi da iƙirarin da ke alaƙanta burinsa da shugaban ƙasa.
“Ba baƙon abu ba ne a ji mutane suna cewa Tinubu ne yake ɗaukar nauyina. Ko lokacin da nake son tsayawa takara da Buhari a 2019, an gaya mini cewa shugaban ƙasa na yanzu ne yake ba ni kuɗi."
“Zan iya gaya muku dalla-dalla a yayin da nake tsaye a gaban ku a yau cewa ban taɓa cin gajiyar ko kobo ɗaya daga gare shi ba. Godiya ga Allah da Asiwaju yake raye har yau. Idan akwai mai hujja, to ya nuna wa duniya. Don haka, ba na damuwa da irin wannan zargi."

Kara karanta wannan
2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar
“Ina bayyana aniya ta da kuma tsayawa takarar wannan tikiti ne saboda kwararan hujjoji da nake da su a zuciyata. Ba a taɓa samuna da wani laifi ba ko kuma aka hukunta ni saboda aikata wani abu da ya shafi ayyukan yaƙi da jam’iyya.”
- Stanley Osifo
Bai tsoron goyon bayan da Tinubu ya samu
Mai neman takarar ya jaddada cewa goyon bayan da shugabannin jam’iyya ke bayarwa ba ya soke tanadin kundin tsarin mulki da ke jagorantar zaɓen ɗan takara, inda ya dage cewa ba zai karaya ba saboda ƙaruwar goyon bayan da Tinubu yake samu a cikin jam’iyyar.

Source: Twitter
Lokacin da aka tambaye shi yadda yake nufin tunkarar tasirin goyon bayan da ake nuna wa shugaban kasar, Osifo ya ce ba zai tsorata ba, shafin Chronicle.ng ya kawo labarin.
“Ba na adawa da gwamnoni ko shugabannin jam’iyya da suke nuna goyon baya ga kowa. Ban fito don faɗa da kowa ba, amma dukkanmu muna da haƙƙi na tsarin mulki mu bi burinmu na siyasa."
“Haka kuma, babu wani sashe na kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu da ya ce idan aka nuna goyon baya ga wani, to kai tsaye shi ne ya zama ɗan takarar jam’iyyar."
"Babu irin wannan dokar, koda a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da ya nuna goyon baya a matsayin hanyar zama ɗan takara."
- Stanley Osifo
An farmaki mai tallata Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mai tallata mawaka, Ijoba Danku, ya tsallake rijiya da baya bayan an farmake shi a Legas.
Ijoba Danku ya bayyana cewa wasu matasa sun kai masa harin saboda goyon bayan da yake nuna wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma jam’iyya mai mulki ta APC.
A cewarsa, harin yana da alaka da siyasa ne kai tsaye da kuma yadda ya tsaya yana tallata Bola Tinubu da APC.
Asali: Legit.ng

