Zaben fidda gwani a Zamfara: Marafa ya goyi bayan hukuncin APC ya ga laifin Yari kan rikicin da ya balle

Zaben fidda gwani a Zamfara: Marafa ya goyi bayan hukuncin APC ya ga laifin Yari kan rikicin da ya balle

Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan man fetur, Sanata Kabiru Garba Marafa ya goyi bayan hukuncin soke zaben fidda gwani na gwamna da kwamitin jam’iyyar APC tayi jiya a jihar Zamfara, duk da cewar shi ne ke kan gaba a dukkanin mazabun da aka gudanar da zaben.

Marafa wanda ya kasance daya daga cikin yan takaran a wata sanarwa ya ga laifin Gwamna Yari kan rikicin da ya balle a wasu yankunan jihar lokacin zaben.

Yace kira ga ci gaba da zaben da Yari da abokan tafiyarsa suka yi duk da rikicin da ya balle rashin tunani ne da rashin hankali da kuma mugunta.

“Yari ya rura huta a jihar don kawai makircin da ya kulla na son tursasawa mutane wanda basa muradi yaayi aiki domin ya cigaba da mulki ta bayan fage bayan ranar 29 ga watan Mayu 2019,” inji shi.

Yace an dage zaben fidda gwanin sau uku sannan cewa bayan tattaunawa daban-daban da hukumomin tsaro, yan takarar gwamna tara, INEC da kuma kwamitin da aka tura daga Abuja a ranar Talata, an amince kan cewa a gudanar da zaben a jiya Laraba, 3 ga watan Oktoba.

Yace jim kadan bayan rarraba kayayyakin zaben, wakilan dan takaran suka sanar da cewa takardun kuri’a basu kai kaso 10 da mambobin jam’iyyar suka yi rijista a mazabarsu ba.

Marafa ya kara da cewa lamarin ya tursasa shugaban kwamitin aika sammaci na taron gaggawa a ofishin kwamishinan yan sanda domin magance lamarin.

“Wadanda suka halarci taron sun hada da sukkanin yan takarar da shugabannin hukumomin tsaro a jihar."

Shugaban ya kira shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole wanda yayi Magana da dukkanin yan takarar daya bayan daya, a karshe yan takaran suka yarda cewa a ajiye batun takardan kuri’ sannan a bi tsarin kato bayan kato ta yadda mutane zasu tsaya a bayan dan takarar da suke muradi.

KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

Yace daga nan sai shugaban jam’iyyar na kasa ya amince da tsarin. Yace daga nan sai aka fara zabe lafiya a wasu mazabu sannan sakamako ya fara fitowa, kawai sai ga rikici ya kaure a manyan biran inda jami’an gwamnati da suka matsu suka shirya yan iska domin su kai hai ga masu zabe musamman mata.

Yace hakan ya sa dole shugaban kwamitin zaben ya dakatar da zaben don dakatar da rikicin.

Kawai sa’o’i bayan dakatar da zaben sai ga Gwamna Yari ya sanar da cewa za’a ci gaba da zaben a yau ba tare da yayi ko jaje ga iyalan wadanda suka mutu da wanda suka ji rauni ba.

Ya kuma bukaci dukkanin magoya bayansa a jihar da su kwantar da hankulansu sannan su bi hukuncin kwatin kasar da kuma jiran sanarwa akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel