Yayin da Ake Zargin APC, Dan Uwan Wike Ya Zama Kwamishinan Zabe a Najeriya
- Hukumar INEC ta sauya wa kwamishinan zabe a jihar yayin da ake shirin gudanar da zaben shekarar 2027
- INEC ta nada dan uwan Nyesom Wike, Anugbum Onuoha a matsayin sabon kwamishinan zabe, yanzu haka ya karɓi ragamar aiki.
- Onuoha, wanda ke da alaƙa da Nyesom Wike, ya taba rike mukamai a gwamnati da kuma kula da zaben Edo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tura Anugbum Onuoha zuwa Akwa Ibom da ke Kudancin Najeriya.
Hukumar ta nada Onuoha wanda ya kasance ɗan uwan ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin sabon kwamishinan zabe na jiha.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta reshen jihar Akwa Ibom ta wallafa a shafinta na Facebook a yau Asabar 25 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani
Ɗan uwan Nyesom Wike ya samu muƙami a INEC
Onuoha ya karɓi ragamar aiki daga hannun tsohon kwamishina Obo Effanga a hedikwatar hukumar da ke Uyo a ranar 17 ga Afrilun 2026.
Kafin wannan nadin, Onuoha ya taba rike mukamin kwamishinan zabe a Edo inda ya jagoranci zaben gwamna na 2024.
Haka kuma ya taba zama mai ba gwamnatin Rivers shawara kan harkokin filaye a lokacin mulkin Nyesom Wike.
Sanarwar ta ce:
"An sauya jagoranci a ofishin INEC na Akwa Ibom, yayin da tsohon Kwamishinan Zaɓe na jihar (REC), Obo Effanga, Esq, ya mika ragamar aiki ga sabon REC, Farfesa Anugbom Onuoha a hedikwatar jihar da ke Uyo ranar Juma’a, 17 ga Afrilu, 2026.
"Farfesa Onuoha masani ne a fannin shari’a, kuma yana da tarin karramawar ilimi a tarihinsa. An turo shi daga Edo, yayin da shi kuma Barista Effanga zai koma can domin ci gaba da aiki, bayan ya taba yin hidima a jihar a baya."

Source: Facebook
Mukamin da kwamishinan ya rike a INEC a baya
An naɗa shi tare da wasu kwamishinonin zabe 10 a shekarar 2023 daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai nadin nasa ya jawo suka daga jama’a bisa zargin yiwuwar son kai saboda alakar siyasa da yake da ita.
A tsarin hukumar INEC, sauya wurin aiki irin wannan abu ne da aka saba yi domin tafiyar da ayyukan cikin gida da inganta harkokin zabe.
Yanzu haka Onuoha zai jagoranci harkokin zabe a Akwa Ibom, jiha da ake yawan fafatawa sosai a siyasa wanda ake zargin an yi nadin ne saboda tasirin Wike da kuma neman hanyar taimakawa APC.
APC ta zabi Fubara kan Wike
Mun ba ku labarin cewa Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya ce rikicin siyasa tsakanin Nyesom Wike da Siminalayi Fubara ba ya cikin hurumin jam’iyyar.
Yilwatda ya bayyana cewa Wike dan jam’iyyar PDP ne, yayin da Fubara ke APC, don haka ba za su tsoma baki ba.
Ya ce batun tsige Gwamnan Rivers al’amari ne na cikin APC, kuma jam’iyyar na da hanyoyin warware irin wadannan matsaloli.
Asali: Legit.ng
