An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe

An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Fati Gombe

- Wata matashiya da ta nemi takarar majalisar jihar Gombe, Fati Gombe ta koka kan yadda wasu a jam'iyyar suka ki tantance ta

- Fati Gombe ta ce rashin amincewa ta bayar da kanta ga wasu gurbatattun jagororin jam'iyyar ya sa ba'a tantance ta ba

- Fati tayi ikirarin wani jigo cikin masu tantancewar ya bukaci da bayar da kanta gareshi ko ta bayar da toshiyar baki na N100,000 idan tana son a tantance ta

Wata mai neman tikitin takarar majalisar jiha a Gombe a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hajiya Fati Gombe ta ce an ki tantance ta domin tsayawa takara a jam'iyyar ne saboda ta ki amincewa wasu gurbatattun shugabanin jam'iyyar suyi lalata da ita.

An hana ni takara a PDP saboda na ki yarda ayi amfani da ni - 'Yar takarar majalisa a Arewa
An hana ni takara a PDP saboda na ki yarda ayi amfani da ni - 'Yar takarar majalisa a Arewa
Asali: Twitter

Fati Gombe wadda mawakiya ce ta bayyana cewar ta cika duk sharrudan takarar amma kwamitin masu tantance 'yan takara tayi mursisi ta ki amincewa da takarar ta ba tare da wasu kwarararan hujjoji ba.

DUBA WANNAN: Saraki ya yi ganawar sirri da dan takarar gwamna na APC na jihar Arewa

"Rashin tantance da kwamitin tayi bai bani mamaki ba saboda akwai daya daga cikin 'yan kwamitin da ya bukaci in same shi a otal ko kuma in bayar da cin hancin N100,000 muddin ina son a tantance ni.

"Ina da shaida saboda lokacin da ya nemi in zo in same shi a otal din nayi amfani da waya ta na dauki maganar kuma nan gaba zan bayyana wa duniya wannan hirar kuma in fadi sunansa," inji Fati.

Mawakiyar wadda ke da gidauniyar tallafawa mata, marayu da sauran marasa galihu da shawarci Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe da uwar jam'iyyar PDP suyi bincike tare da magance gurbatattun da ke jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel