An fara kira APC ta gudanar da sabon zaben ‘Dan takarar Gwamna a Abia da Yobe

An fara kira APC ta gudanar da sabon zaben ‘Dan takarar Gwamna a Abia da Yobe

Mun samu labari cewa Umar Ali wanda yana cikin wadanda su ka nemi takarar kujerar Gwamnan Jihar Yobe a Jam’iyyar APC ya nuna cewa bai amince da sakamakon zaben APC da aka yi ba kwanan nan.

An fara kira APC ta gudanar da sabon zaben ‘Dan takarar Gwamna a Abia da Yobe
‘Yan takarar Gwamna sun rubutawa Shugaban APC takarda a soke zabe
Asali: Depositphotos

Malam Ali ya bayyana cewa an yi magudi kiri-kiri a zaben fitar da ‘Dan takarar Gwamna wanda Alhaji Mai Mala Buni yayi nasara. ‘Dan takarar yace su na da hujjoji har na bidiyo da ke nuna cewa an murde zaben na fitar da gwani.

‘Dan takarar ya kuma bayyana cewa ba ayi amfani da takardun zaben da aka amince da su daga Hedikwatar Jam’iyya ba wanda hakan ya bada dama aka tsaida Sakataren APC na kasa a matsayin ‘Dan takarar Gwamnan Jihar.

KU KARANTA: Wani Sanatan Yobe ya sha kasa a zaben fitar da gwani na PDP

A Jihar Abia ma dai an samu wannan kukan inda Prince Ikonne Paul wanda ya sha kashi a zaben da aka yi na tsaida ‘Dan takarar Gwamna ya rubutawa Shugaban APC na kasa Adams Oshimhole takarda yana neman a sake zabe.

Prince Ikonne wanda da su aka kafa APC ya nemi ayi sabon zabe domin kuwa an yi magudi a wancan zaben da aka yi kamar yadda ya fada da bakin sa. A Jihar Yobe dama dai Gwamnan ya nuna fifiko kan Mai Mala Buni.

A baya kun ji cewa rikici ya barke a Gabashin Jihar Neja bayan zaben fitar da gwani da Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar inda Sanatan da ke wakiltar Yankin David Umaru ya kama hanyar shan kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel