Jam'iyyar APC na neman kakaba wani ‘Dan uwan Buhari a matsayin ‘Dan Majalisan Daura

Jam'iyyar APC na neman kakaba wani ‘Dan uwan Buhari a matsayin ‘Dan Majalisan Daura

- APC na neman mikawa wani ‘Dan uwan Shugaba Buhari tikitin Majalisa

- Masu neman takara a Yankin Daura sun dai nuna cewa ba za su yarda ba

Jam'iyyar APC na neman kakaba wani ‘Dan uwan Buhari a matsayin ‘Dan Majalisan Daura
APC na iya rasa kujerar Daura a Majalisar Tarayya a 2019
Asali: UGC

Mun samu labari daga Jaridar DAILY NIGERIAN cewa Mutanen Yankin Daura da Mai’Adua da kuma Sandamu sun yi zanga-zanga a dalilin kakaba masu wani ‘Dan uwan Shugaban Kasa Buhari da ake neman yi a matsayin ‘Dan takara.

Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar nan ta dage sai ta ba Fatihu Muhammad tikitin takarar kujerar Majalisar Tarayya a zaben 2019. Sai dai jama’a sun nuna cewa ba su tare da wannan mataki da APC ke nema ta dauka da karfin tsiya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai kawu yake wajen wannan ‘Dan takaran da APC ke neman tsaidawa a matsayin ‘Dan Majalisar Tarayya. ‘Dan takarar bai da farin jini kuma wasu su na ganin cewa APC za ta sha kasa idan tayi hakan.

KU KARANTA: Jami'an DSS na neman kawowa zaben Buhari cikas a 2019

Salisu Daura wanda yana cikin masu neman kujerar ya ja hankalin Jam’iyyar da su guji yin wannan ‘danyen aiki ko APC ta sha kasa. Daura yace manyan APC na kokarin ganin an tsaida wannan ‘Danuwan Shugaban kasan a zaben da za ayi.

Masu neman kujeran a APC dai sun hada da Salisu Daura, Aminu Jamu da kuma Kabir Abdullahi wanda su ka nuna cewa ana neman nuna masu karfin dangi da kuma karfa-karfa inda su ka nuna cewa sam ba za su amince da hakan a APC ba.

Kun san cewa tsohon ‘Dan Majalisar Yankin na Daura-Maiadua-Sandamu watau Farfesa Umar Adamu Katsayal yana cikin masu neman kujerar Sanata Yankin Katsina ta Arewa a Jam’iyyar ta APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel