Duk wanda aka kama yana lika naira a wajen biki zai tafi gidan yari – Kwamitin ma’aikatan banki
Wadanda ke lika kudi naira a wajen biki dab suke da tafiya gidan yari, kwamitin ma’aikatan baki tayi gargadi a jiya, Alhamis, 4 ga watan Oktoba.
A cewarta za’a samar da kotun tafi da gidanka da zata dunga maganin masu wofantar da kudin kasar.
Da suke gargadi bayan taronsu a Lagas, kwamitin ma’aikatan bakin yace za’a tura kotun tafi da gidanka a fadin kasar domin ta yi maganin masu yin sakaci wajen kula da kudin kasar.
Kakakin babban bakin Najeriya (CBN) Isaac Okorafor yace yan sanda da ma’aikatar shari’a zasu kasance a cikin aikin.
A cewarsa idan mutun na rawa yana lika kudi zai tafi gidan yari ne daga wajen taron, domin wakilan tsaro na nan suna jira don kama duk wanda ya karya doka.
KU KARANTA KUMA: Yan takara 3 sun ki amincewa da zaben fidda gwanin yan majalisar wakilai na APC a Daura
Da yake shawartan yan Najeriya kan yadda zasu yi kyautar kudi yace: “Idan kana so ka ba mai bikin kudi, kasanya shi ciki takardan wasika sannan ka ba mai bikin. Ku sani duk wanda aka kama yana talla sannan yana rubutu akan naira zai fuskanci daurin watanni bakwai a gidan yari ko ya biya N50,000 koma dukka biyun.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng