An Gano Sakon da Matashi Ya Tura Wa Iyalansa kafin Kai Wa Shugaban Amurka Hari
- Bincike ya fara nisa kan mutumin da ake zargi da kai hari wurin taron liyafa da shugaban Amurka, Donald Trump ya halarta
- Hukumomin Amurka sun gano wata rubutacciyar wasika da wanda ake zargi, Cole Tomas ya aika wa iyalansa kafin kai harin
- Wannan hari dai ya ja hankalin duniya musamman saboda Shugaba Trump na wurin, tuni dai aka gurfanar da Tomas a kotu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Hukumomin Amurka sun fara bincike kan wani sako da wanda ake zargi da yunkurin kai hari kan Shugaba Donald Trump, ya turawa iyalinsa.
Bayanai sun nuna cewa an gano wata wasika da ake zargin Cole Tomas Allen, matashin malamin makaranta mai shekaru 31 daga California, ya aikawa iyalansa kafin kai harin.

Source: Getty Images
Jaridar Trubune Nigeria ta rahoto cewa matashin ya yi harbe-haren bindiga a wurin taron masu dauko rahoton White House, wanda Shugaba Trump ya halartar a Washington DC.
Wasikar da matashin ya tura ga iyalansa
A cewar bayanai, Allen ya aika wa iyalansa wasika kafin harin, inda ya fara da neman afuwa bisa abin da ya kudarta aikatawa.
“Bari na fara da neman gafara ga duk wanda na ba kunya game da amincewar da ya mini,” in ji wani bangare na wasikar.
Rahotanni sun nuna cewa ya bayyana fushinsa matuka, yana mai cewa yana niyyar kai hari kan jami’an gwamnati, duk da cewa bai sa ran samun gafara ba daga yan uwansa ba.
Yadda matashin ya halarci wurin taron
An ce wanda ake zargin ya tashi daga Los Angeles zuwa Chicago, sannan ya wuce Washington DC, inda ya sauka a otel din da ake gudanar da taron wanda ya samu halartar Shugaba Trump da wasu manyan jami’an gwamnatin Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa ya zo da makamai guda biyu, bindiga kirar 38-calibre da kuma bindiga mai harsashi 12-gauge, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.
Ana zargin ya yi kokarin wuce tsaro kafin ya bude wuta, inda ya harbi jami’in tsaron daya da ke sanye da rigar kariya kafin a cafke shi.
Amurka ta gurfanar da shi a kotu
Mukaddashin Antoni Janar na Amurka, Todd Blanche, ya ce har yanzu suna kokarin gano dalilin harin, amma bincike na farko ya nuna cewa mutumin ya yi kiyyar farmakar gwamnati ne.
An gurfanar da wanda ake zargin kan tuhume-tuhume biyu na amfani da bindiga da kuma laifin kai hari kan jami’in gwamnati da makami mai hatsari.
Sai dai, jami’an tsaro sun ce wanda ake zargin ya ki bada hadin kai yayin binciken da ake gudanarwa.

Source: Getty Images
Rahotanni sun nuna cewa Allen ya kasance yana furta kalamai masu tsauri bayan shiga harkokin fafutukar siyasa a Los Angeles, inda daga baya ya mallaki makamai kuma ya rika atisaye a wuraren harbi.
Hukumomi sun ace wannan hali ne daga baya ya rikide zuwa kai wannan harin da ya janyo hankalin duniya.
Dalilin yawan kai wa Shugaba Trumo hari
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya yi magana game da yawan hare-hare da matasa dauke da bindigu ke yunkurin kai masa.
Trump ya ce yana kallon hare-haren a matsayin wata alama ta irin tasirin da yake da shi, yana mai cewa ba zai bari irin wannan barazana ta tsoratar da shi ba.
Shugaban kasar ya bayyana cewa ko a jikinsa, kuma ya jaddada cewa ba zai bari irin waɗannan hare-hare da ke auna rayuwarsa, su hana shi aiki ba.
Asali: Legit.ng


