Zaben cikin gida: 'Yan takara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da zabe a Kano

Zaben cikin gida: 'Yan takara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da zabe a Kano

- 'Yan takarar majalisar wakilai na jam'iyyar PDP reshen jihar Kano sunyi zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben

- 'Yan takarar sunyi ikirarin cewa an tafka magudin zabe kana an tursasa musu 'yan takarar da basu lashe zaben ba

- Anyi kokarin ji ta bakin kwamitin shirya zaben fidda gwanin da shugaban jam'iyyar na Kano amma basu ce uffan ba

Dimbin masu neman takarar kujerar majalisar wakilai na tarayya karkashin jam'iyyar PDP sunyi zanga-zanga a kan tursasa musu 'yan takara da saba dokokin zabe a zaben fidda gwani da jam'iyyar tayi a Kano.

'Yan takarar daga kananan hukumomi 44 da ke jihar sunyi tattaki har zuwa Prince Hotel inda Kwamitin Korafi na zaben ke zauna inda su kayi korafin cewa an tafka magudi kuma an tursasa musu 'yan takarar da basu so.

Zaben cikin gida: 'Yan takara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da zabe a Kano
Zaben cikin gida: 'Yan takara sunyi zanga-zangar rashin amincewa da zabe a Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan majalisar APC ya koma PDP bayan rasa tikitin takara

Abdullahi Ramat, daya daga cikin masu neman tikitin takarar kujerar majalisar wakilai na mazabar Ungogo/Minjibir ya ce bai amince da zaben Tajo Zaura da akayi a matsayin dan takarar jam'iyyar ba.

"Kwamitin gudanar da zaben basu tuntube ni ba domin fada min inda za a gudanar da zaben fidda gwanin. Daga baya na samu labari sun tafi gidan dan takarar da suke so domin gudanar da zaben.

"Mutanen da suka zabe shi ba wakilan jam'iyyar bane, hasali ba 'yan jam'iyyar mu bane. Wannan karara ya sabawa dokar zabe," inji Mr Ramat.

Bayan mazabar Ungogo/Minjibir an kuma samu labarin barkewar rikici a wasu mazabun kamar Nasarawa, inda Abba Bposs da Umar Yakasai suka ki amincewa da zaben Ado Hotoro a matsayin dan takarar jam'iyyar.

Kazalika, an samu irin wannan matsalar a mazabar Gwale inda sauran 'yan takarar suka ce basu amince da zaben Yusuf Babangida a matsayin wanda ya lashe zaben ba inda suka ce Nasiru Dandago ne ya lashe zaben.

Premium Times ta tuntubi kwamitin shirya zaben don jin ta bakinsu amma basu ce uffan ba kuma duk yunkurin da akayi na kirar shugaban riko na jam'iyyar a Kano, Jamilu Danbatta ya ci tura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel