2019: Hafizu Kawu ya samu tikitin takarar Majalisa a Jam’iyyar APC

2019: Hafizu Kawu ya samu tikitin takarar Majalisa a Jam’iyyar APC

NAIJ Hausa ta samu labari cewa Kwamared Hafiza Kawu ya samu tikitin takarar kujerar Majalisar Tarayya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki inda zai nemi ya wakilci Yankin Tarauni a zaben 2019.

2019: Hafiza Kawu ya samu tikitin takarar Majalisa a Jam’iyyar APC
Kwamared Kawu zai yi takarar kujerar Majalisar Tarayya a APC
Asali: UGC

Kwamared Hafiz Kawu ya tika ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Tarauni a Majalisa Honarabul Nasiru Babale Ila a zaben fitar da gwanin da aka yi jiya inda ya samu kuri’a 56, 076 inji Malamin aikin zaben na Jam’iyyar APC.

Hon. Nasiru Babale Ila shi ne ke kan kujerar ta Yankin Mazabar Taurauni a yanzu haka. Ila dai ya samu kuri’u kadan ne a saman 13, 000 inda ya zo na uku a zaben da aka yi. Ibrahim Suleyman ne ya zo na biyu da kuri’u 16, 131.

KU KARANTA: Sanatan Katsina ta tsakiya ya rasa tikitin ‘Dan Majalisan APC ya zo na 3

‘Yan takara 5 ne dai su ka shiga zaben sai dai shi Hafiz Kawu wanda yana cikin Hadiman Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne yayi nasara a zaben inda aka yi amfani da tsarin kato-bayan-kato a Kano.

A baya kun ji labari cewa Sanata Kabiru Gaya ya doke Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkar Majalisa watau Kawu Sumaila a zaben fitar da gwani na Kano ta Kudu. Sai dai an koka da cewa an tafka magudi a zaben.

Jiya mu ka ji cewa 'Dan takarar Shugaban Kasa Aminu Tambuwal ya gana da Obasanjo. Hakan na zuwa ne bayan Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara wajen wani tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Ahmadu Ali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel