'Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini da Iyalansa a Plateau

'Yan Bindiga Sun Hallaka Malamin Addini da Iyalansa a Plateau

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci wanda ya jawo asarar rayuka a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wani fasto tare da wasu daga cikin iyalansa a yayin harin da suka kai cikin dare
  • Lamarin ya kara sanya tsoro a zukatan mazauna yankunan da aka kai harin, inda wasu daga cikinsu suka bar kwana a gidajensu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Gako da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe wani fasto da wasu daga cikin iyalinsa guda uku a yayin harin da suka kai a cikin dare.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 26 ga watan Afirilun 2027.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan bayin Allah a Katsina, an samu asarar rayuka

'Yan bindiga sun kashe fasto da iyalansa

Waɗanda abin ya shafa an bayyana sunayensu kamar haka, Fasto Ayuba Choji, matarsa Chundung Ayuba, da kuma yayansu biyu, Cyril Ayuba da Endurance Ayuba.

Maharan sun far wa ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka harbi ba kakkautawa.

Wata mazauniyar yankin, Martha Dalyop, ta shaida wa manema labarai cewa ƙarar harbin bindigar ya tursasa wa mazauna garin gudu don tsira da rayukansu.

Mutane na barin gidajensu a Plateau

Ta yi kukan cewa hare-haren da ake yawan kai wa sun ci gaba da jefa al’ummomi cikin tsoro, har ta kai da da yawa ba sa iya kwana a gidajensu ko kula da gonakinsu.

Jaridar The Punch ta ce yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar matasan Berom, Rwang Tengwong, ya siffanta lamarin a matsayin abin ban tsoro.

“Wannan hari na baya-bayan nan ya nuna cewa maharan yanzu suna kai hari ne a wuraren shaƙatawa, yankunan manoma, da kuma jami’an tsaro na 'yan sa-kai da ke kare karkara."

Kara karanta wannan

Yana ajiye mukamin minista, Tuggar ya fadi abin da ya jawo ta'addanci a Bauchi

- Rwang Tengwong

'Yan bindiga sun rarrabu yayin harin

Ya yi zargin cewa maharan sun rarraba kansu gida-gida ne yayin gudanar da aikin, inda wasu suka kai hari kan mazauna gari, wasu suna lalata gonaki, yayin da wani rukunin ke yin sintiri ko tare hanyoyi don hana mutane tserewa ko samun taimako.

Haka kuma, Tengwong ya bayyana cewa maharan sun lalata gonakin kabeji, barkono, da masara da dama a garin Kassa da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

Wannan sabon lamari ya ƙara ruruta wutar fargaba a faɗin Riyom da maƙwabciyarta Barkin Ladi, inda mazauna yankin ke kiran hukumomin tsaro da na gwamnati da su tsananta ƙoƙari don dakatar da kashe-kashe da lalata hanyoyin samun abinci a jihar.

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, da na rundunar ’yan sandan jihar Plateau, SP Alabo Alfred, ba su amsa saƙon da aka aika musu ta WhatsApp ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun takura da hare hare, mutane da dama sun bar gidajensu a Sokoto

Al’ummar Berom sun sha zargin Fulani makiyaya da alhakin kai waɗannan hare-haren, amma shugaban ƙungiyar MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya sha musanta waɗannan zarge-zargen, yana mai dagewa cewa mambobinsa ba su da hannu a hare-haren da ake kai musu.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wani kauye na jihar Katsina.

Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka akalla mutane 10 a harin wanda suka kai a garin Gurbi da ke karamar hukumar Kankara.

'Yan bindigan sun iso ne suna harbi ba kakkautawa, sai dai dakarun sa-kai na yankin da wasu mazauna gari masu ɗauke da makamai sun tunkare su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng