Hormuz: Iran Ta Miƙa Sabon Tayin Sulhu ga Amurka, An Tabo Batun Makamin Nukiliya

Hormuz: Iran Ta Miƙa Sabon Tayin Sulhu ga Amurka, An Tabo Batun Makamin Nukiliya

  • Bayan ta ja kafa na ƴan kwanaki, Iran ta fara nuna alamun don a koma teburin tattaunawa da Amurka don a sasanta rikicin yankin
  • Daga cikin abin da ta fara yi shi ne mika sabon tayin sulhu ga Amurka domin buɗe mashigar Hormuz da sojojin Amurka suka yi wa tsinke
  • Daga cikin abin da sabon tayin ya ƙunsa akwai jinkirta tattaunawar nukiliya har sai an ɗage takunkumin da Amurka ta ƙaƙabawa Iran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Iran – Iran ta gabatar wa Amurka da wani sabon shiri na sulhu wanda ya haɗa da jinkirta tattaunawar nukiliya, a wani yunƙuri na sake buɗe mashigar ruwan Hormuz da kuma kawo ƙarshen yaƙin da ke gudana.

A cewar rahoton, an isar da tayin ne ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan, inda Iran ke neman a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta domin ba ɓangarorin damar kaiwa ga sulhu na dindindin.

Kara karanta wannan

Iran ta kafa tarihi a duniya bayan shiga kwana na 57 a yakinta da Isra'ila

Iran ta mika sabuwar bukata ga Amurka
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian da takwaransa na Amurka Donald Trump Hoto: Masoud Pezeshkian/Donald Trump
Source: Getty Images

Wani jami’in Amurka da wasu majiyoyi biyu sun tabbatar wa da kafar Axios cewa an mika wannan sabon daftari da ke kunshe da bukatun Iran game da bude Hormuz.

Iran za ta dawo teburin sulhu da Amurka

Al-Jazeera ta wallafa cewa shirin ya tanadi cewa tattaunawar nukiliya za ta zo ne a gaba, bayan Amurka ta ɗage takunkumin da ta kakaba kan mashigar Hormuz, da ke da matuƙar muhimmanci wajen jigilar mai a duniya.

Rahoton ya ce masu shiga tsakani daga Pakistan sun riga sun miƙa wannan tayin ga fadar White House, sai dai har yanzu babu tabbacin ko Amurka za ta amince ta tattauna a kai.

A gefe guda, ana sa ran Shugaban Amurka, Donald Trump, zai jagoranci wani muhimmin taro a ranar 27 ga Afrilu, 2026 a dakin kula da harkokin tsaro na fadar White House, tare da manyan jami’an tsaro da na harkokin ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Hormuz: Matakin Amurka da Iran ya ta'azzara farashin fetur a duniya, ganga ta haura $100

Iran: Donald Trump zai yi ganawar sirri

Wata mai magana da yawun fadar White House, Olivia Wales, ta bayyana cewa batun Iran na daga cikin sahun tattaunawar sirri da Trump zai yi.

Ta ce:

"Waɗannan muhawarori ne masu matuƙar muhimmanci, kuma Amurka ba za ta yi tattaunawa ta kafafen yaɗa labarai ba.”

Ta ƙara da cewa Amurka za ta tabbatar da duk wata yarjejeniya da za ta amfanar da al’ummarta, tare da jaddada cewa ba za ta taɓa yarda Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Iran ta ce babu batun nukiliya a halin yanzu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian Hoto: Anadolu
Source: Facebook

A halin yanzu, duka Iran da Amurka na ci gaba da kulle mashigar Hormuz, lamarin da ya sa ta zama kusan ba za a iya bin ta ba, wanda ya haifar da fargaba a kasuwannin duniya, musamman wajen safarar mai.

An soka ganawar Amurka da Iran

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya dakatar da tafiyar wakilansa zuwa birnin Islamabad, lamarin da ya soke zaman tattaunawa da Iran.

Kara karanta wannan

'Ƙarfi ya ci,' Iran ta yi abin mamaki da jiragen dakon mai 3 suka shiga Hormuz

Trump ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne saboda yadda ake ta kwan-gaba kwan-baya kan shirya zagaye na biyu na zaman sulhu da aka shirya a Islamabad.

Bayanai sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya bar birnin Islamabad bayan ganawa da jami'an Pakistan Duk da cewa Amurka ta aika da jami'anta can.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng