Sanatocin Arewa 3 sun dauki zafi bayan sun rasa tikitin komawa majalisa

Sanatocin Arewa 3 sun dauki zafi bayan sun rasa tikitin komawa majalisa

Yayinda sanatoci uku daga jihar Niger suka rasa kudirinsu na yin tazarce inda sabbin shiga suka lashe zaben fidda gwani na samun tikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sanatocin sun dauki zafi inda suka yi zargin cewa anyi amfani da karfin kudi da kuma yan daba a tsarin zaben fidda gwanin.

A zaben fidda gwani na ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba, Sani Musa ya sanar da wadanda suka yi nasara, a Niger ta gabas, sanata mai ci David Umaru ya sha kaye, a Niger ta kudu, Sanata Mustapha Mohammed ne kashin baya a wurare hudu da ka kammala inda ake jiran karamar hukuma guda yayinda Hon. Ibrahim Ebbo, Alhaji Mohammed Nina Enagi da Malik Cheche ke kan gaba yayinda a Niger ta arewa, kakakin majalisar dattawa Sanata Sabi Abdullahi Abiyu ya sha kashI a hannun Jon Zakeri Jikantoro.

Sakamakon haka, sanatocin sun dau zafi sannan sunyi zargin cewa anyi magudi a zaben fidda gwanin wanda a cewarsu ya sabama chanji da yaki da rashawar da APC ke tsaye a kai.

Sanatocin Arewa 3 sun dauki zafi bayan sun rasa tikitin komawa majalisa
Sanatocin Arewa 3 sun dauki zafi bayan sun rasa tikitin komawa majalisa
Asali: UGC

Sanata mai wakiltan Niger ta gabas a majalisar dokokin kasar, Sanata David Umaru ya ki amincewa da sakamakon zaben fidda gwanin na APC inda ya bayyana shirin a matsayin ba gaskiya ba.

David Umaru ya bayyana hakan a jiya a wata hira da maneema labarai inda yace lallai ba’a gudanar da zaben yadda yakamata ba cewa cike yake da rashin adalci, rikici da kuma siyan kuri’a.

KU KARANTA KUMA: Sabon rikici ya kunno kai a APC: An ruro ma Oshiomhole wuta cewa yayi murabus daga matsayinsa

A cewarsa anyi amfani da yan daba don suyi ma magoya bayansa duka da kuma korarsu tare da hana su yin zabe.

Ya kuma yi kira ga masu fada a ji a APC da suyi watsi da sakamakon zaben sannan su sake sabon zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel