'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Bayin Allah a Katsina, an Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani kauye na jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
- Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba bayan sun fuskanci turjiya yayin harin da suka kai
- 'Yan bindigan dai sun kashe mutanen ne cikin rashin imani lokacin da suka yi kokarin tsira da rayukansu daga harin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun hallaka aƙalla mutane 10 yayin da wasu da dama suka ji rauni a wani harin ta’addanci da da aka kai a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kashe mutanen ne a harin da suka kai a garin Gurbi da ke ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa 'yan bindigan waɗanda aka fi sani da ’yan fashin daji, sun far wa yankin ne a yammacin ranar Lahadi, 26 ga watan Afirilun 2026.
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Katsina
'Yan bindigan sun iso ne suna harbi ba kakkautawa, sai dai dakarun sa-kai na yankin da wasu mazauna gari masu ɗauke da makamai sun tunkare su.
Mazauna yankin sun bayyana cewa mutanen garin da 'yan sa-kai sun hana ’yan ta’addan shiga cikin garin, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
Garin Gurbi wani yanki ne na manoma da ’yan kasuwa a Kankara, kuma yana iyaka da wasu kauyuka da ke cikin haɗari a yankin Tsafe na jihar Zamfara.
Wani shugaban matasa a garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:
“’Yan bindigan sun fara harbi ne kafin su ƙaraso cikin garin, lokacin da mambobinmu na sa-kai suka ji karar harbi, sai suka fita wajen gari don tunkarar su."
“Saboda tsoron abin da ka iya zuwa ya koma, mutane da dama sun gudu daga gidajensu don kada a ritsa da su. Lokacin da ’yan bindigan suka ga mutanenmu suna gudu, sai suka bi su a baya suka fara harbinsu."
An kashe bayin Allah
Wani ma’aikacin lafiya a yankin wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an kashe wasu daga cikin mutanen ne bayan an harbe su daga kusa.
“Ina jin wasu daga cikin mazauna garin sun yi karo da ’yan bindigan ne yayin da suke ƙoƙarin gudu daga garin, inda ’yan fashin suka harbe su ba tare da imani ba,”
in ji ma’aikacin lafiyar.
Mazauna yankin sun gano cewa an kashe wasu daga cikin mutanensu ne kawai bayan ’yan ta’addan sun ja da baya.
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abubakar-Sadiq Aliyu, ya shaida wa manema labarai cewa zai ba da bayani daga baya kan batun harin.
“Ku yi haƙuri. Zan dawo gare ku nan ba da jimawa ba, don Allah."
- DSP Abubakar Sadiq-Aliyu
'Yan bindiga sun harbi tsohon kwamishina
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon kwamishinan harkokin addini a Zamfara, Sheikh Abdullahi Maharazu Mafara, ya gamu da harin ƴan bindiga.
Malamin wanda dan siyasa ne ya tsallake rijiya da baya bayan wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka bude masa wuta.
Maharan da ke dauke da makamai sun bude wuta sau da dama kan motarsa, lamarin da ya jawo ya jikkata a kafarsa amma bai rasa ransa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


