Matakan da Gwamnati Ta Dauka da Aka Samu Bullar Annobar COVID 19 a Najeriya
- Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Legas (LSPHCB) ta tabbatar da cewa matakan kariya da dakile yaduwar cututtuka (IPC) na ci gaba da aiki a jihar
- Sakataren gwamnati a ma'aikatar, Dr. Ibrahim Mustafa, ya bayyana cewa an dauki matakai yayin da aka samu bullar cutar COVID-19 a jihar Cross River
- Ya sanar da cewa a halin yanzu magungunan rigakafin cutar COVID-19 sun kare a fadin kasar Najeriya, amma gwamnatin tarayya ta riga ta dauki mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas – Hukumar LSPHCB ta ba wa mazauna jihar Legas tabbacin cewa cibiyoyin lafiya na matakin farko ba su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsabta da kariya daga cututtuka masu yaduwa.
Dr. Ibrahim Mustafa ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na NAN, inda ya ce tsarin da aka kafa tun lokacin annobar COVID-19 ya zama ruwan dare a yanzu.

Kara karanta wannan
Babban lauya ya hango haramci a shari'a da sojojin da suka shirya kifar da Tinubu

Source: Twitter
Gwamnati ta fita neman rigakafin COVID-19
Dangane da halin da ake ciki game da sake bullar cutar, Dr. Mustafa ya shaida wa NAN cewa:
"Ba za mu iya cewa COVID-19 ta bar mu gaba daya ba. Abin da ya canza shi ne yawan allurar rigakafi ya kara wa mutane garkuwar jiki, wanda hakan ya sanya cutar ba ta yin tsanani idan ta kama mutum."
Sakataren ya bayyana cewa a halin yanzu magungunan rigakafin cutar COVID-19 sun kare a fadin Najeriya baki daya.
Ya ce an riga an karar da wadanda ake da su, amma gwamnatin tarayya tana kokarin sake shigo da sababbin alluran domin jama'a su ci gaba da samun damar yin rigakafi da zarar sun isa.
Ya jaddada cewa yawan alluran da aka yi wa mutane a baya ya taimaka kwarai wajen rage kaifin yaduwar cutar a cikin al'umma, in ji rahoton Daily Trust.

Source: Original
Matakan kariya a cibiyoyin lafiya
Hukumar ta ce matakan IPC ba na COVID-19 kadai ba ne, har ma da sauran cututtuka masu yaduwa ta hanyar kwayoyin cuta da bidis. Manyan matakan da ake amfani da su sun hada da:
- Tabbatar da wanke hannu akai-akai da sabulu ko amfani da sinadarin sanitizer.
- Wajibi ne ga duk wanda yake nuna alamun mura ko tari ya sanya takunkumin fuska.
- Ma'aikatan lafiya dole su sanya safar hannu ga kowane mara lafiya daya sannan su zubar da ita bayan amfani.
Dr. Mustafa ya ja kunne kan cewa sassauci wajen bin wadannan matakan na iya janyo barazana ga lafiyar jama'a, don haka ya bukaci ma'aikata da marasa lafiya da su ci gaba da bin dokokin tsabta domin kare kansu da wasu.
Dan China ya dawo da COVID 19 a Najeriya
Tun da fari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da bullar cutar Covid-19, inda wani dan kasar China mai shekaru 53 ya kamu da cutar wanda ya daga hankulan al'umma.

Kara karanta wannan
Ningi: Babban kuskuren da zai hana wasu sanatoci da 'yan majalisu koma wa kujerunsu a 2027
Sanarwar gwamnati ta tabbatar da cewa hakan ya faru ne bayan ɗan China ya dawo Najeriya daga kasarsa ta haihuwa.
Kwamishinan lafiya a Cross River, Dakta Henry Ayuk, ya ce an gano cutar bayan an dauki samfurin majiyyacin a asibitin koyarwa na Calabar.
Asali: Legit.ng
