Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai fiye da 23 a Makarantar Islamiyya

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Sace Dalibai fiye da 23 a Makarantar Islamiyya

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai 23 da matar mai makaranta bayan sun farmaki wani gidan marayu hade da makarantar islamiyya a Kogi
  • Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto ɗalibai 15 daga cikin waɗanda aka sace jim kaɗan bayan harin, yayin da ake ci gaba da fafatawa domin ceto sauran
  • Gwamnatin Kogi ta bayyana cewa makarantar na gudanar da ayyukanta ba bisa ƙa'ida ba a cikin daji ba tare da yin rajista ko sanar da hukumomin ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kogi – Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 23 da kuma matar mai makaranta bayan sun kai hari wani gidan marayu dake hade da makaranta a yankin Zariagi da ke Lokoja, jihar Kogi.

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a daren Lahadi, inda maharan suka farmaki makarantar addinin Musuluncin da aka bayyana sunanta da Dahallukitab Group of Schools.

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan daba sun kai farmaki fitacciyar kasuwar wayoyin hannu a jihar Kano

'Yan bindiga sun sace dalibai da suka kai hari makarantar marayu a Kogi
Yara 'yan makaranta suna dibar ruwan alwala. Hoto: OLYMPIA DE MAISMONT/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

'Yan bindiga sun kai hari makarantar marayu

Wannan hari ya haifar da tashin hankali a yankin yayin da maharan suka kwashe yaran zuwa cikin daji, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun mayar da martani cikin gaggawa, inda hakan ya kai ga samun nasarar ceto ɗalibai 15 daga cikin waɗanda aka sace.

Fanwo ya jinjina wa ƙoƙarin jami'an inda ya ce:

"Gwamnatin jihar Kogi tana jinjina wa bajinta da ƙwarewar jami'an yan sanda da sauran jami'an tsaro wajen kawo ɗauki cikin lokaci domin tunkarar wannan lamari."

Gargadi kan gudanar da makarantu a daji

A yayin da yake ƙarin bayani kan yanayin makarantar, kwamishinan ya bayyana cewa makarantar tana gudanar da ayyukanta ne ba tare da bin ƙa'idodin gwamnati ba.

Kara karanta wannan

An tafka asara: Yadda Iran ta lalata manyan kadarorin Amurka a Gabas Ta Tsakiya

Ya bayyana cewa gudanar da makaranta ko gidan marayu a wuraren da suke da nisa da jama'a ko kuma a cikin daji ba tare da sanar da hukumomi ba babban haɗari ne ga tsaro.

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin Kogi, Fanwo ya ce:

"Wannan makaranta ana gudanar da ayyukanta ne ba bisa ƙa'ida ba a cikin daji, ana yin hakan ba tare da rajista da gwamnatin jiha ba, kuma ba tare da sanin hukumomin tsaro da da suka dace ba."
Jami'an tsaro sun fara ceto wasu daga cikin daliban da aka sace a makarantar marayu da ke Kogi
Taswirar jihar Kogi, inda 'yan bindiga suka sace marayu da ke karatu a wata makarantar Islamiyya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Matakin da jami'an tsaro suka dauka

A halin yanzu, ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an ceto sauran mutane takwas da matar mai makarantar waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwar.

Gwamnati ta bayyana cewa ba za ta huta ba har sai ta ga an kamo waɗanda suka kai wannan hari tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Fanwo ya buƙaci dukkan masu gudanar da makarantu da gidajen marayu da ke wuraren da ke da haɗari da su tuntuɓi hukumomi domin tantance yanayin tsaron wurarensu akai-akai, musamman a wannan yanayi na tsaro da ake ciki.

'Yan bindiga sun je sace dalibai Kogi

Kara karanta wannan

Mutanen gari sun cire tsoro, sun yi gaba da gaba da yan bindiga a Katsina

A wani labari, mun ruwaito cewa, mutum biyu sun rasa rayukansu lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari makarantar Kiri da ke Aiyetoro Kiri.

'Yan ta'addan sun kai harin ne a safiyar ranar Laraba, inda mafarauta da ‘yan sa-kai suka dakile harin kafin ‘yan bindigar su samu damar sace ɗalibai.

Shugaban karamar hukumar Kabba Bunu, Barista Zacheus Dare, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da gidan talabijin din ta wayar salula.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com