"Sun Mutu": Obasanjo Ya Faɗi Abin da zai Hana Matatun NNPCL Aiki har Abada
- Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce matatun man gwamnatin Najeriya ba za su sake aiki ba
- Ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan an fara raɗe-raɗin cewa wasu ƴan damfara za su yi gwanjon kayan matatun
- Tsohon shugaban ya bayyana cewa kamfanin Shell ya ƙi karɓar tayin sarrafa matatun domin su dawo cikin hayyacinsu
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ogun– Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya sake jaddada cewa matatun man fetur mallakin NNPCL ba za su sake yin aiki yadda ya kamata ba.
Obasanjo ya bayyana cewa ba za a samu kan matatun ba duk da kokarin neman haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu da gwamnati ke yi.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa Obasanjo ya ce ya dade yana gargadi kan cewa tsarin gwamnati kadai ba zai iya tafiyar da irin wadannan manyan ayyuka ba.
Olusegun Obasanjo ya yi magana kan matatun Najeriya
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Olusegun Obasanjo ya ce kamfanoni sun ki amincewa da tayin gwamnatin tarayya na aiki tare wajen farfaɗo da matatun.
A cewarsa:
“Daya daga cikin darussan da na koya shi ne cewa haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (PPP) yana aiki. Ka duba Nigeria LNG Limited, inda masu zaman kansu ke da 51% , gwamnati kuma ke da 49% — wannan shi ne kadai aikin da gwamnati ba ta lalata ba.”
Obasanjo ya bayyana yadda ya nemi kamfanin Shell da ya karɓi 10% na hannun jari ko kuma ya gudanar da matatun, amma suka ƙi amincewa.
Ya ce:
“Na roƙe su su zo su tafiyar da matatun, amma suka ce a’a.”
Dalilin kamfanoni na gudun matatun NNPCL
Obasanjo ya ƙara da cewa wani babban jami’in Shell ya ba shi dalilai huɗu da suka sa suka ki amincewa da tayin gwamnati na sayen hannun jari matatunta.

Kara karanta wannan
Kwana ya kare: Daga fitowa motsa jiki, tsohon 'dan wasan Najeriya ya rasu a Kaduna
Na farko, ya ce ribar su mafi yawa tana fitowa ne daga bangaren hako mai ba daga tacewa ba. Na biyu, ya ce matatun Najeriya ƙanana ne idan aka kwatanta da na duniya, inda ake da ƙarfin tace gangar mai 250,000 zuwa 300,000 a rana.

Source: Facebook
Na uku, rashin kulawa da ingantaccen gyara ya lalata su. Na huɗu kuma, ya ce akwai yawan cin hanci da rashawa a tsarin matatun.
Tsohon shugaban ya kuma tuna yadda attajirin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya bayar da Dala miliyan 750 domin mallakar 51% na wasu matatun guda biyu.
Sai dai ya ce magajinsa, marigayi Umaru Musa Yar'Adua, ya soke yarjejeniyar saboda matsin lamba daga kamfanin mai na kasa, NNPCL.
Ya ce:
“Na gaya masa cewa NNPC ba za ta iya tafiyar da matatun ba, ya ce ya sani, amma matsin lamba ne ya sa ya yarda.”
Obasanjo ya ƙara da cewa an kashe kusan Dala biliyan 16 wajen gyaran matatun, duk da cewa wannan ya kusan kai kuɗin da Dangote ya kashe wajen gina babbar matatar mai mafi girma a Afrika.
An saka wasu kayan NNPCL a kasuwa?
A baya, mun wallafa cewa kamfanin mai na kasa, NNPCL ya yi bayani game da rahotannin da ke cewa an fara sayar da ƙarafa da sauran tarkacen matatunsa.
Sanarwar da aka fitar da ta ce kamfanin ya ce akwai alamu ƴan damfara na shirin zaluntar bayin Allah da sunan NNPCL wajen sayar masu da kayan matatun ba bisa ka'ida ba.
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bukaci jama'a a rika kai rahoto ga hukumomin tsaro idan an gamu da irin wadannan mutane da ke shiga rigarsa don cutar jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

