Mutanen Gari Sun Cire Tsoro, Sun Yi Gaba da Gaba da Yan Bindiga a Katsina

Mutanen Gari Sun Cire Tsoro, Sun Yi Gaba da Gaba da Yan Bindiga a Katsina

  • Mazauna garin Gurbi da ke ƙaramar hukumar Kankara a Katsina sun yi tsayin daka wajen hana 'yan bindiga shiga garinsu, amma mutum 10 sun rasa rayukansu
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kasa shiga cikin garin, sai suka farmaki mutanen da ke guduwa daga yankin, inda suka harbe su har lahira
  • Duk da gargadin da mazauna suka bai wa jami’an tsaro kafin harin, ba a samu dauki ba sai bayan an kashe mutane kuma aka fara kwashe gawarwaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Mazauna ƙauyen Gurbi da ke ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina sun yi nasarar hana 'yan bindiga kai hari.

Mazauna garin sun haka maharan kutsa kai cikin garinsu bayan sun fito domin kare al’ummarsu daga harin.

An yi artabu da ƴan bindiga a Katsina
Taswirar jihar Katsina da fama da matsalolin tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

An yi artabu da ƴan bindiga a Katsina

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ta'asa, sun hallaka ministan tsaron Mali yayin hari a gidansa

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa maharan sun iso tun da yamma, amma mutanen gari sun taru domin hana su shiga, cewar Daily Trust.

Ya ce bayan da maharan suka kasa shiga cikin garin, sai suka juya kan mutanen da ke tserewa daga yankin, inda suka harbe su daga kusa.

A cewarsa, sama da mutum 10 ne aka kashe a yankin Nagodi, wani ƙauye da ke gaban Gurbi, sannan daga bisani aka dawo da gawarwakin zuwa Gurbi.

Mazaunin ya kuma bayyana takaicinsa kan yadda suka sanar da jami’an tsaro tun bayan samun bayanan shirin harin, amma ba a samu martani ba.

Ya ce jami’an tsaro sun isa ne kawai bayan an kashe mutane, inda suka fara taimakawa wajen kwashe gawarwakin waɗanda aka rasa.

Wata majiya daga fadar shugaban al’ummar Gurbi ta tabbatar da cewa maharan sun gaza shiga cikin ƙauyen saboda juriyar da mazauna suka nuna.

Majiyar ta ƙara da cewa maharan sun kai hari ne kan mutanen da suka firgita suka fara guduwa domin ceton rayukansu daga harin.

Yan gari sun dakile harin ƴan bindiga a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina. Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda.
Source: Facebook

Yadda ƴan bindiga suka addabi yankin Kankara

Kara karanta wannan

Cole Allen: Abubuwan mamaki game da matashin da ya kai hari kan su Donald Trump

Kankara na daga cikin wuraren da hare-haren 'yan bindiga suka sake ƙaruwa a Katsina cikin 'yan kwanakin nan, lamarin da ke ƙara tada hankalin jama'a.

Kwanaki uku da suka gabata ma, 'yan bindiga sun kai hari a Zangon Kankara inda suka ƙone gidaje biyu da mota guda tare da sace mutum biyu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar 'yan sanda ko ofishin kwamishinan harkokin tsaro na Katsina.

Rahoton ya bayyana cewa ana ci gaba da bibiyar bayanai kan wannan hari, yayin da al’umma ke jiran matakin hukumomi game da lamarin.

Yan bindiga sun harbi tsohon Kwamishina

Mun ba ku labarin cewa wani tsohon kwamishina a Zamfara,m ya tsallake rijiya ta baya bayan wani mummunan harin ƴan bindiga.

An ce Sheikh Abdullahi Maharazu Mafara ya gamu da tsautsayi bayan ‘yan bindiga sun bude masa wuta a hanyar zuwa taron APC.

Lamarin ya faru ne yayin da yake tafiya daga Talata Mafara zuwa Gusau domin halartar taron APC, inda aka yi masa kwanton bauna tare da harbe-harbe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com