Yan takara 3 sun ki amincewa da zaben fidda gwanin yan majalisar wakilai na APC a Daura

Yan takara 3 sun ki amincewa da zaben fidda gwanin yan majalisar wakilai na APC a Daura

- Yan takara uku sun ki amincewa da zaben fidda gwanin yan majalisar wakilai na APC a Daura

- Yan takarar sune Alhaji Daura Salisu, Alhaji Aminu Jamu da kuma Alhaji Kabir Abdullahi

- Suna neman tikitin wakiltar mazabar Daura/Maiadua/Sandamu a majalisar wakilai

Yan takara uku a karkasin jam’iyyar All Progressives Congress aspirants (APC) dake neman kujerar majalisar wakilai a yankin Daura/Maiadua/Sandamu, mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yammacin ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba sunyi watsi da zaben fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar don zabar wanda zai wakilce ta a zaben 2019.

Yan takarar sune Alhaji Daura Salisu, Alhaji Aminu Jamu da kuma Alhaji Kabir Abdullahi.

Yan takara 3 sun ki amincewa da zaben fidda gwanin yan majalisar wakilai na APC a Daura
Yan takara 3 sun ki amincewa da zaben fidda gwanin yan majalisar wakilai na APC a Daura
Asali: Facebook

Da suke Magana a taron manema labarai a Daura, sunyi zargin cewa gwamnatin jihar Katsina da manyan jam’iyyar na son daura zabin ransu.

Sun yi kira ga ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato don zabar dan takarar da zai wakilci jam’iyyar a zaaben majalisar wakilai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: APC ta saki jerin sunayen yan takarar gwamna 24 da ta amince da su (cikakken sunayensu)

Yan takarar sun kuma bayyana cewa zasu yi amfani da karfin doka wajen kwatar yancinsu sannan sun bukaci magoya bayansu da su kwantar da hankulansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng