Babban taron PDP: Wakilai sun mamaye yan chanji

Babban taron PDP: Wakilai sun mamaye yan chanji

Kasuwa ta bude ma ýan chanji dake kasuwanci musamman a wajaje dake kusa da babban Hotel din Port Harcourt inda abubuwa suka rinchabe masu sakamakon daruruwan kwastamomi da suka mamaye su wadanda ake zargin wakilan PDP ne.

Sun mamaye su suna ta chanjin kudade a wajen su, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa wani mai chanjin kudaden waje a kusa da babban hotel din, Musda Danladi yace ya yi ciniki da mutane sama da 50 da misalin karfe 4:00pm na ranar Juma’a, 5 ga watan Oktoba.

Babban taron PDP: Wakilai sun mamaye yan chanji
Babban taron PDP: Wakilai sun mamaye yan chanji
Asali: Depositphotos

Yace mutanen da ake zargin wakilan jam’iyyar ne na ta tunkararsu a kokarinsu na chanjin kudade.

KU KARANTA KUMA: Babban taron PDP: Karya ne ban janye ba - Saraki

“Tun safe muna ta samun mutane da ake ganin wakilan PDP. Suna ta zuwa da yawa don chanja kudade daga wurinmu. Kasuwancin yayi dadi sosai kuma muna addu’a ya ci gaba da kasancewa haka,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel