Miyagun 'Yan Daba Sun Kai Farmaki Fitacciyar Kasuwar Wayoyin Hannu a Jihar Kano

Miyagun 'Yan Daba Sun Kai Farmaki Fitacciyar Kasuwar Wayoyin Hannu a Jihar Kano

  • 'Yan daba sun kai hari kan 'yan kasuwa da abokan cinikinsu a kasuwar sayar da wayoyin hannu ta Farm Center da ke jihar Kano
  • Wani rahoto ya nuna cewa 'yan dabar sun fito ne daga wurin wani taron siyasa, inda suka daka wa wayoyin wawa da tsakar rana yau Litinin
  • Dakarun rundunar 'yan sanda sun kai dauki tare da tarwatsa maharan, amma har yanzu babu wata sanarwa daga hukumomi a hukumance

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari fitacciyar kasuwar sayar da wayoyin hannu watau Farm Center da ke cikin kwaryar birnin jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa harin da 'yan dabar suka kai ya haddasa firgici tsakanin ‘yan kasuwar da ke gudanar da harkokinsu a Farm Center tare da abokan cinikayyar su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka malamin addini da iyalansa a Plateau

Farm Center.
Mutane sun yi cincirindo a kasuwar Farm Center bayan harin 'yan daba a Kano Hoto: Daily Nigerian Hausa
Source: Facebook

Yadda aka kai hari Farm Center

Jaridar Tribune Nigeria ta ruwoito cewa shaidun gani da ido sun ce maharan sun kutsa kasuwar da rana tsaka yau Litinin, inda suka rika dukan jama’a tare da amfani da makamai masu kaifi domin tsoratar da su.

An ce harin ya fi shafar yankin Yoyo Plaza, wani bangare na kasuwar da aka fi gudanar da harkokin sayar da wayoyi.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kwashe wayoyin hannu da sauran kayayyaki daga hannun ‘yan kasuwa, kwastomomi da ma masu wucewa a kusa da wurin.

Rahotanni da ba a tabbatar da su ba, sun nuna cewa wasu daga cikin maharan sun fito ne daga wani taron siyasa da aka gudanar a Kano ta Tsakiya, sai dai babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da hakan.

Matakin da jami’an tsaro suka dauka

Daga bisani, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin, inda suka tarwatsa maharan tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasuwar ta Farm Center.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace dalibai fiye da 23 a makarantar islamiyya

Wata majiya a kasuwar ta shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa, ana zargin ƴan daban sun halarci wani taron siyasa da aka yi a yankin, kafin su farmaki wajen siyar da wayar da ke Yoyo Plaza.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Majiyar ta kara da cewa, ƴan daban sun daka wawa tare da kai sara ga ƴan kasuwar dake tsaka da ciniki, haka kuma, sun dinga kwacewa mutane wayoyinsu a kan hanya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu tabbacin mutuwar kowa, amma an ce mutane da dama sun samu raunuka

Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba tukuna, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Mahara sun kashe mutum a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a Karamar Hukumar Rogo a Jihar Kano.

An ruwaito cewa maharan sun kashe mutum guda tare da jikkata wasu da dama, lamarin da ya sa aka kara tsaurara matakan tsaro a yankin.

Maharan sun wuce zuwa ofishin kungiyar ‘yan sa-kai na yankin inda suka rika harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, wanda ya tilasta wa mazauna yankin tserewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262