Gwamna Fintiri Zai Fafata da Babban Dan Kasuwa kan Kujerar Sanata a Zaben 2027

Gwamna Fintiri Zai Fafata da Babban Dan Kasuwa kan Kujerar Sanata a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu a shekarar 2027
  • Alamu sun nuna cewa gwamnan zai fito takarar kujerar sanata ta Adamawa ta Arewa a karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki
  • Gwamna Fintiri zai fafata da shahararren dan kasuwa wanda ya koma siyasa, Abdulrahaman Kwacam domin samun tikitin APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - An samu kwararan alamu da ke nuna za a fafata a fagen siyasa tsakanin Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da fitaccen ɗan kasuwa wanda ya koma harkar siyasa, Abdulrahaman Kwacham.

Manyan mutanen biyu za su fafata ne kan kujerar sanatan mazaɓar Adamawa ta Arewa a zaɓen 2027.

Gwamna Fintiri zai yi takara a 2027
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce abokan siyasa da magoya bayan Kwacham sun dakatar da zirga-zirga a tsohon garin kasuwanci na kan iyaka wato Mubi a ranar Alhamis, 23 ga watan Afirilun 2026 yayin da suka tarbe shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Abdulrahaman Kwacam zai yi takarar sanata

Wannan biki ya zama wata babbar alama ta shirye-shiryensa na shiga takarar sanata domin wakiltar mazaɓarsa a majalisar dattawa.

Yayin da yake jawabi a wurin taron, Abubakar Inuwa, wani mataimakin kwanturola na hukumar shige da fice mai ritaya, ya ce Kwacham ya ba da gudummawa mai yawa wajen ci gaban garin Mubi.

Ya jaddada rawar da Kwacham ya taka wajen samar da damarmakin ayyukan yi da dama a sassa masu zaman kansu da na gwamnati ga matasan yankin.

Inuwa ya bayyana cewa al’umma sun daɗe suna kira ga Kwacham da ya amsa “kiran da ya zama dole,” tare da yin amanna cewa salon shugabancinsa na canji zai tabbatar da cewa mazaɓar ta samu wakilcin da ya dace.

Shin Fintiri da Kwacam za su iya daidaitawa?

Ya tabbatar da cewa ziyarar da suka kai wa Sarkin Mubi, Alhaji Abubakar Isah Ahmadu, ta kasance ne domin neman albarkar masarauta ga wannan tafiya.

Kara karanta wannan

Yusuf Tuggar, ministan Tinubu da ya yi murabus ya ayyana shiga takarar gwamna

Inuwa ya lura cewa sasantawa da fahimtar juna ne kawai za su iya warware takaddamar burin siyasa na Kwacham da Gwamna Fintiri; idan ba haka ba, za a raba gardama ne a zaɓen fitar da gwani kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya tanada.

An yi gangamin nuna goyon baya ga Fintiri

A daidai lokacin kuma, wata haɗakar ƙungiyoyin matasa, ’yan kasuwa, da ’yan siyasa daga ƙananan hukumomi biyar na Adamawa ta Arewa sun gudanar da gangamin nuna goyon baya, suna kiran Gwamna Fintiri da ya tsaya takarar wannan kujera.

Gwamna Fintiri zai fafata a zaben 2027
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri Hoto: @GovernorAUF
Source: Twitter

A gangamin da aka yi ranar Asabar a Mubi, waɗannan ƙungiyoyi sun bayyana gwamnan a matsayin “magajin da ya dace” na kujerar, inda suka siffanta shi a matsayin wakili wanda aka gwada kuma aka amince da shi domin shekarar 2027.

Duka Fintiri da Kwacham mambobi ne na jam’iyyar APC mai mulki, kuma yayin da kowane ɓangare ke amanna cewa ɗan takararsa ya fi gogewa da ƙwarewa, masu sharhin siyasa suna ganin lokaci ne kawai zai nuna wanda zai yi nasara a ƙarshe.

Gwamna ya yi alkawari ga Tinubu kan 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi babban gangami domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu da Gwamna Nasir Idris a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa Kebbi tana tare da Tinubu, yana mai danganta hakan da ayyukan ci gaba da aka aiwatar a jihar.

Ya ce yawan jama’ar da suka halarta shaida ce cewa al’ummar Kebbi suna tare da APC, yana mai jaddada cewa kuri’unsu za su tafi ga jam’iyyar a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng