Dan majalisar wakilai ya sake samun tikitin takara a PDP karo na 4 a Sokoto
Wani dan majalisar wakilai da ya shafe zango uku a majalisar, Isa Bashir-Kalanjeni ya sake samun tikitin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) takarar kujerar mazabar Tangaza/Gudu a jihar Sokoto a zaben 2019.
Bashir-Kalanjeni, wanda ya kasance dan takara guda, ya zamo baida abokin hamayya a ranar Alhamis, 4 ga watan Oktoba.
Jami’in zaben, Malam Usman Yabo ne ya kaddamar da nasarar nasa bayan wakilai sun tabbatar da shi, kamfanin dillancin labarai ta ruwaito.

Asali: UGC
Yabo a wata sanarwa yace wakilan jam’iyyar 207 ne suka tabbatar da Bashir Kalanjeni a matsayin dan takara kamar yadda doka ta tanadar.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Shettima ya lashe tikitin takarar sanata a APC
Da yake jawabin godiya Bashir-Kalanjeni ya yabama wakilai da sauran magoya bayan jam’iyyar kan goyon bayan da suka bashi, sannan yayi alkawarin yiwa mazabar shi hidima ta fannin lafiya, ilimi da sauransu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng