2027: Atiku Ya Yi Gargadi kan Neman Hana Kamfen a Jihohin Arewa 8

2027: Atiku Ya Yi Gargadi kan Neman Hana Kamfen a Jihohin Arewa 8

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi gargadi game da fara maganar hana yakin neman zabe a wasu jihohin Arewa
  • Ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da wani uzuri ba wajen tauye hakkin jama'a na shiga harkokin dimokuradiyya a 2027
  • An fara maganar hana yakin neman zabe a wasu jihohin Najeriya ne saboda yadda ake kara samun hare-haren 'yan ta'adda a cikinsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi gargadi kan yunkurin dakatar da yakin neman zabe a wasu sassan Arewacin Najeriya.

Ya yi magana yana mai cewa hakan na iya tauye hakkin kundin tsarin mulki da kuma kara fargabar hana jama’a damar kada kuri’a a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tsananta.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama mai taimaka wa yan bindiga su samu kudi a Sakkwato, ya fara bayani

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Atiku Abubakar yayin taron 'yan adawa a jihar Oyo. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa martanin Atiku ya biyo bayan rahotannin da ke cewa majalisar dattawa na nazarin yiwuwar dakatar da harkokin siyasa a jihohi takwas da ke fama da karuwar tashe-tashen hankula.

Gargadin Atiku kan hana kamfen

Game da neman hana kamfen a wasu jihohi, Atiku ya ce lamarin abin damuwa matuka, yana mai cewa duk da cewa rashin tsaro babbar matsala ce, bai kamata a yi amfani da ita wajen takaita shiga harkokin dimokuradiyya ba.

Ya ce:

“Ya kamata a bayyana karara cewa hakkin kada kuri’a da shiga cikin tsarin zabe hakki ne na asali wanda ba za a iya tauye shi ba.
“Duk wani yunkuri, ko a bayyane ko a boye, na dakile harkokin siyasa a wasu sassan Arewacin Najeriya zai haifar da damuwar hana jama’a damar kada kuri’a.”

Zargin rage kada kuri'a a Arewa

Atiku ya tuna da wasu bayanan sirri na baya da ke nuna yiwuwar kokarin rage yawan masu kada kuri’a a wasu jihohin Arewa, yana mai cewa abubuwan da ke faruwa a yanzu na kara tabbatar da irin wannan fargaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano da makamai cikin dare, sun yi kisa

Tribune ta rahoto ya ce:

“Wannan ba batun yakin neman zabe kadai ba ne; ya shafi wakilci, hadin kai, da kuma mutunta dimokuradiyyarmu. Ba za a magance rashin tsaro ta hanyar toshe muryoyin jama’a ba,”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa al’ummar Arewa, kamar sauran ‘yan Najeriya, suna da hakkin samun tsaro da kuma cikakkiyar damar shiga harkokin dimokuradiyya.

Atiku Abubakar da 'yan ADC yayin zanga-zanga a Abuja
Yadda Atiku Abubakar da manyan ADC suka yi zanga-zanga a Abuja. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Kira a samar da tsaro a Arewa

Ya kara da cewa alhakin gwamnati ne ta tabbatar da tsaro, kamar yadda ya kamata a bar ‘yan kasa su yi amfani da hakkokinsu na kasa ba tare da tsoro ko tsangwama ba.

“A lokacin da jama’a ke fama da matsin rayuwa da rashin tsaro, mafi karancin abin da gwamnati za ta yi shi ne ta tabbatar da an saurari muryoyinsu, ba ta hana su ba.
"Duk wata manufa da za ta nuna ana ware wasu yankuna za ta kara haifar da rashin yarda da rarrabuwar kawuna,”

Kara karanta wannan

2027: Kano da wasu jihohin Arewa 7 da majalisa ke son haramta wa yin kamfen

Maganar hana kamfe a jihohi 8

A wani labarin, mun kawo muku cewa a makon da ya gabata, Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi dubi kan kamfen a wasu jihohi takwas.

Sanata Ningi ya yi gargadin cewa karuwar tashin hankali na bukatar daukar matakan gaggawa da suka wuce tattaunawa na yau da kullum da ake yi.

Jihohi ake maganar dakatar da harkokin siyasa a cikinsu sun hada da Borno, Plateau, Bauchi, Benue, Niger, Sokoto, Kebbi da wasu sassan jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng