Wata Mata Ta Haihu a tsakiyar Mutane a Taron Matar Gwamna, An ba Ta Kyautar Miliyoyin Naira
- Wata matar aure ta haifi 'yan biyu a wurin taron siyasa da uwargidar gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Nasir Idris ta shirya a Birnin Kebbi
- Gwamna Nasir Idris ya samu halartar wannan taro tare da wasu manyan jami'an gwamnatin Kebbi, 'yan majalisa da mambobin APC
- An ruwaito cewa nakuda ta riski matar a wurin taron, kuma ta haihu a nan kafin daga bisani a dauke ta zuwa asibiti don kula da lafiyarta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi, Nigeria - Wata mata ta haifi jarirai maza tagwaye a wurin wani taron siyasa da uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Zainab Nasir Idris, ta shirya a birnin Kebbi
Matar gwamnan ta shirya wannan taro ne domin tara kudade da nufin tallafa wa kungiyoyin mata a fadin jihar Kebbi.

Source: Facebook
Wata mata ta haihu a taron siyasa
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a filin wasa na Haliru Audu da ke Birnin Kebbi, inda matar ta fara naƙuda cikin taron mata kafin daga bisani ta haihu a wurin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Taron ya samu halartar gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, tare da uwargidansa da wasu mambobin jam’iyyar APC mai mulki.
Mai jego ta samu kyautar N5m
Bayan sanar da haihuwar, dan majalisar wakilai mai wakiltar Suru/Bagudo, Hon. Bello Dallatun Ka’oje, ya bayar da gudummawar Naira miliyan biyar ga matar domin kula da lafiyarta da kuma bikin suna, a madadin gwamnan Kebbi.
Rahotanni sun nuna cewa matar ta je taron ne domin neman tallafi, amma sai ta shiga naƙuda kuma ta haifi tagwayen jarirai maza.
Daga bisani, an dauki matar tare da jariran zuwa asibiti mafi kusa domin ci gaba da kula da lafiyarsu.

Kara karanta wannan
Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027
A tara kudi, kayan tallafawa mata a Kebbi
Game da makasudin taron kuwa, Dhugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kebbi, Faruk Enabo, ya bayar da gudummawar turamen atamfa guda miliyan daya domin rabawa ga kungiyoyin mata a bikin Babbar Sallah.
Bugu da kari, ya sanar da bayar da tallafinkudi Naira miliyan 30 ga matan a madadinsa da abokan aikinsa.

Source: Facebook
Muhimmancin mata a siyasa
Enabo ya bayyana cewa mata na taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da kasuwanci, inda ya ce su ne ginshikin nasarar zabe.
Ya kara da cewa za su ci gaba da kokarin inganta rayuwar mata kamar yadda gwamna Nasir Idris ke yi, kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro.
A karshe, an tattara sama da naira miliyan 200 a taron domin tallafa wa kungiyoyin mata a fadin jihar Kebbi.
Kebbi ta jaddada goyon baya ga Tinubu
A wani labarin, kun ki cewa jam’iyyar APC a Kebbi ta shirya gagarumin gangamin hadin kai na mutum miliyan daya domin nuna goyon baya ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Gangamin ya samu halartar magoya bayan jam’iyyar daga kananan hukumomi 21, inda Gwamna Nasir Idris ya jagoranci jaddada goyonn jihar Kebbi ga tazarcen Shugaba Tinubu a 2027.
Da yake jawabi, Gwamna Idris ya bayyana cewa Kebbi tana tare da Tinubu, yana mai danganta hakan da ayyukan ci gaba da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

