Kwankwaso, Peter Obi Sun Samu Tayin Tikitin Takara Kai Tsaye a Zaɓen 2027

Kwankwaso, Peter Obi Sun Samu Tayin Tikitin Takara Kai Tsaye a Zaɓen 2027

  • Jam’iyyar NDC ta tura roko na musamman ga tsohon yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
  • NDC ta roke su da su sauya sheka daga ADC zuwa gare ta domin fafatawa zaɓen 2027, tare da ba su damar tikitin shugaban ƙasa
  • Rikicin shugabanci da ke addabar ADC da kuma jadawalin INEC na gabatar da sunayen ‘yan takara ya ƙara jefa jam’iyyun adawa cikin matsin lamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar NDC ta roƙi Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da manyan jiga-jigan ADC da su koma cikinta domin fafatawa zaɓen 2027 mai zuwa.

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin shugabanci ya addabi ADC da kuma jadawalin hukumar zabe ta INEC.

An yi wa Kwankaso da Obi ta yin takara
Sanata Rabiu Kwankwaso da tsohon gwamna, Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

An yi wa Kwankwaso, Obi tayin takara

Kara karanta wannan

2027: Obidients na zargin masoya Abba da ƙoƙarin yi wa tafiyar Obi da Kwankwaso kishiya

A wani saƙo da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na X, ta nuna cewa akwai wa’adin makonni biyu kacal ga Obi da Kwankwaso su shiga cikinta domin samun tikitin shugaban ƙasa.

Jam’iyyar ta ce:

“Abin da muke buƙata a yanzu shi ne kawai. Muna da makonni biyu zuwa lokacin ƙarshe,” inda ta haɗa da hoton musabaha tsakanin Obi da Kwankwaso tare da rubutun “Najeriya za ta daidaita”.

A makon da ya gabata, magoya bayan ‘yan siyasar biyu sun ƙaddamar da wani shiri mai suna “OK Movement” domin tattara goyon baya ga yiwuwar haɗin takararsu a zaɓen 2027 mai zuwa.

Daga baya, Justin Ijeh, sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, ya sanar da nada mambobi a majalisar zartarwa ta ƙasa da kuma tsarin shiyya da jihohi.

Siyasar 2027 ta fara sauya salo kan takarar Kwankwaso da Obi
Jagoran siyasar Kwankwasiyya, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Rikicin da ADC ke fuskanta

Sai dai kuma jam’iyyar ADC na fuskantar rikicin shugabanci wanda ke barazana ga damar ta na shiga zaɓen 2027 yadda ya kamata.

A ranar 22 ga Afrilu, kotun koli ta ajiye hukunci kan ƙarar da bangaren David Mark ya shigar dangane da shari’ar da Nafiu Bala, shugaban wani ɓangare na jam’iyyar, ya kawo.

Kara karanta wannan

2027: An fara tsoron sanatan APC zai raunana aikin Tinubu bayan gana wa da Atiku Abubakar

A gefe guda, Hukumar INEC ta sanya ranar 30 ga Mayu, 2026 a matsayin ranar ƙarshe da jam’iyyu za su gabatar da rajistar mambobinsu da sunayen ‘yan takara don zaɓen 2027.

A ranar Asabar, jam’iyyun adawa sun buƙaci INEC da ta tsawaita lokacin gudanar da zaɓen fidda gwani zuwa ƙarshen watan Yuli.

Jam’iyyun da suka haɗa da ADC karkashin David Mark, wani ɓangare na PDP da Kabiru Turaki ke jagoranta, da kuma NNPP sun ce jadawalin INEC yana ƙoƙarin tauye musu damar fafatawa yadda ya kamata.

Obidients sun zargi masoyan Abba Kabir

An ji cewa kungiyar OK Movement ta ce Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso za su tsaya wa jam'iyyar ADC takara a 2027.

Shugaban ƙungiyar a Abuja, Jabir Ibrahim Yaro ya shaida cewa tafiyarsu ta samu albarkar Sanata Kwankwaso da Obi.

Ya kuma zargi wasu tsofaffin ‘yan Kwankwasiyya da ƙoƙarin kawo ruɗani a tafiyar inda suka kirkiro KO a shafukan sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.