Sabon Salo: APC Ta Faɗi Tsari 2 da Za Ta Yi Amfani da Su wajen Zaɓen Ƴan takara

Sabon Salo: APC Ta Faɗi Tsari 2 da Za Ta Yi Amfani da Su wajen Zaɓen Ƴan takara

  • Jam'iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom ga duk masu sha'awar yin takara a zaben 2027 daga ranar Asabar, 25 ga Afrilu, 2026
  • Jam'iyyar ta fitar da jadawalin gudanar da zabukan fitar da gwani, inda za a gudanar da na shugaban kasa a ranar 23 ga Mayu, 2026
  • APC za ta yi amfani da tsarin zaɓen kato-bayan-kato ko kuma sulhu, amma jam'iyyar ta fadi abin da zai faru idan matsala ta taso

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana shirye-shiryenta na tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

APC ta sanar da cewa za ta fara sayar da fom ɗin tsayawa takara ga mambobinta daga ranar Asabar mai zuwa, 25 ga Afrilu, 2026.

Jam'iyyar APC ta sanar da fara sayar da fom ga masu sha'awar yin takara.
Shugaban APC na kasa, Prof. Nentawe Yilwatda ya na jawabi a ofishin jam'iyyar a Abuja. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

2027: Jam'iyyarAPC za ta fara sayar da fom

Kara karanta wannan

An buga gangar siyasar 2027: INEC ta ba jam’iyyu wa'adin fitar da 'yan takara

Mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Durosinmi Meseko, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, a cewar rahoton Daily Trust.

Durosinmi Meseko ya jero shirye-shiryen ne bayan taron kwamitin gudanarwa (NWC) na APC karo na 186 da aka gudanar a Abuja.

Mataimakin sakataren ya bayyana cewa sayar da fom ɗin takara zai ci gaba har zuwa ranar 2 ga watan Mayu 2026, yayin da 4 ga watan ke zaman ranar ƙarshe ta mayar da cikakkun takardun.

Tantance 'yan takara da zaɓukan fitar da gwani

Jam’iyyar ta fitar da takamaiman ranaku domin tantance masu neman tsayawa takara da kuma gudanar da zaɓukan fitar da gwani kamar haka:

  • Za a tantance masu neman takarar gwamna da na majalisu tsakanin 6 zuwa 8 ga Mayu, yayin da za a tantance masu neman takarar shugaban kasa a ranar 9 ga Mayu.
  • Za a yi zaɓen fitar da gwani na majalisar wakilai a ranar 15 ga Mayu, majalisar dattawa ranar 18 ga Mayu, sannan na majalisun jihohi ranar 20 ga Mayu.
  • Za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na gwamna a ranar 21 ga Mayu, sannan a rufe da na shugaban kasa a ranar 23 ga Mayu, 2026.

Kara karanta wannan

APC ta sa ranar zaɓen fitar da gwani, ta saka N100m na neman takarar shugaban kasa

Tsarin zaben fitar da 'yan takara a APC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Meseko ya musanta rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta ware fom ɗin ga wasu zaɓaɓɓun mutane.

Jam'iyyar APC za ta yi amfani da tsarin kato-bayan-kato da sulhu wajen zaben 'yan takara.
Gungun magoya bayan APC a wani gangamin jam'iyyar da aka gudanar a jihar Imo a Fabrairun 2023. Hoto: @GoziconC
Source: Twitter

Ya bayyana cewa:

"Kofar sayen fom ɗin takara a buɗe take ga dukkan mambobin APC masu sha'awar tsayawa takara. Babu wata iyaka ko hani ga kowa."

Game da salon zaɓen kuwa, jam’iyyar ta bayyana cewa za ta yi amfani da tsarin kato-bayan-kato ne ko kuma yarjejeniyar sulhu.

Sai dai ta bayar da gargaɗin cewa idan har aka tafi kan tsarin sulhu amma ɗan takara ɗaya bai amince ba, to dole za a koma zaɓen kato-bayan-kato domin tabbatar da adalci.

A ƙarshe, jam’iyyar ta tabbatar da cewa ta riga ta miƙa sabon jerin sunayen mambobinta ga hukumar INEC, kuma tana shirye tsaf domin gudanar da zaɓukan.

Tinubu ya gana da gwamnonin APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Bayan sauya shekar Kwankwaso, wasu manyan jiga jigan siyasar Najeriya za su koma ADC

An tsara taron da farko ne da karfe hudu na yamma a dakin majalisar ministoci, amma daga baya aka mayar da shi zuwa dakin taron ofishin shugaban kasa.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar PGF, Hope Uzodimma na Imo, Inuwa Yahaya na Gombe, da Farfesa Babagana Zulum na Borno.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com