Kwamishiniya a Gombe ta tika kawunta da kasa a zaben cikin gida na PDP

Kwamishiniya a Gombe ta tika kawunta da kasa a zaben cikin gida na PDP

- Kwamishina Ilimi na jihar Gombe, Aishatu MB Ahmad ta doke kawunta, Samaila Mu'azu Hassan a zaben fidda gwani na takarar dan majlisar wakilai

- Samaila Mu'azu Hassan dai shine dan majalisa mai wakiltan mazabar Akko da ke jihar Gombe a majalisar wakilai na tarayya

- Aisha ta samu kuri'u 83 yayinda kawunta bai bamu ko kuri'a daya ba

Kwamishinan Ilimi na jihar Gombe, Hajiya Aishatu MB Ahmad ta kayar da kawunta, Samaila Mu'azu Hassan, wanda shine dan majalisa mai wakiltan mazabar Akko a majalisar wakilai na tarayya a zaben fidda gwani na PDP a jihar Gombe.

Yan gida daya sunyi takara: Kwamishina ta doke kawunta a zaben cikin gida
Yan gida daya sunyi takara: Kwamishina ta doke kawunta a zaben cikin gida
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani

Ta samu tikitin takarar ne bayan ta fafata da kawunta, Mu'azu Hassan da wasu 'yan takarar guda uku ciki har da Ciyaman din karamar hukumar Akko, Adamu Jani da Yahaya Saidu Kumo, dan shugaban yakin neman zaben Atiku Abubakar, Sanata Saidu Umar Kumo.

Asihatu ta samu kuri'u 83, Jani Bello ya samu kuri'u 6 yayin da kawunta, Mu'azu Hassan da Yahaya Saidu basu samu ko kuri'a daya ba.

Sai dai kafin a bayyana sakamakon zaben, Mu'azu Hassan ya garzaya gidajen rediyo inda ya sanar da cewar ya janye taka takarar zaben.

A jawabin da tayi bayan nasarar lashe zaben, Aisha ta yi alkawarin samarwa al'umman mazabarta wakilci mai inganci idan ta lashe zabe a babban zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel